|
|
|
Dutse ga wanda bai santa ba, da jin ance Dutse sai Mutum ya yi tunanin gari ne da yake kewaye ko cike da Duwatsu. Shi kuwa wanda ya san ta sai ya shiga alamta ta da su Asarki ko Tandu ko Dutsen Sama ko Dutsan Lalloki ko Warga ko Karakallo ko Falanke da su Gizirawa da sauransu. Wadannan wurare ne da suka kewaye Unguwar Garu inda masarautar Dutse take zaune. Mai karanta wannan bayani zai ga dalilin da ya sa ake cewa Dutse Dutse Gadawur da yadda tsarin zamantakewar mutanen Dutse yake wajen zaman lafiya da rashin tashin hankali da irin rikon amanarsu. Halayyar da tasa tun farko ake yi wa mutanen Dutse lakabin da mutane masu zaman lafiya. Domin haka nema ya sa da aka samu Jihar Jigawa ake yi mata lakabi da sabon wuri mai zaman lafiya. Har wayau kuma za a ga Tarihin Dutse ya fara tun karni na goma sha biyar (15) wajejen 1450AD. Lokacin mulkin Sarkin Kano Abdullahi Barja Sarkin Kano na goma sha shida (16) a mulkin Hausawa ake ganin an kafa Dutse amma akwai rubutaccen Tarihin Dutse da ya nuna cewa garin ya kafu ne a shekara ta 1727M. Haka kuma an kawo tarihin shugabanci a Dutse yadda ya fara tun shekarar 1727M. Sannan da bayanin rayuwar Sarkunan Dutse daki-daki tun daga Dattijon da ake kira Tsohon Mutum har ya zuwa lokacin da shugabancin Dutse ya fita daga hannun Kanawa watau Hausawa ya koma hannun wasu Fulani guda biyu masu kamar “yan biyu da ake kira Musa da Salihi, wadanda suka fara sarauta a shekara ta 1804M. daf da fara jihadin Usman dan Fodiyo. Watakila, mai karanta wannan bayani ya yi mamakin ganin mutumin Dutse ya je ya mulki mutanen Gwarzo a yamma da Kano ko kuma mutumin Yola ta cikin Birnin Kano ya zo ya mulki Dutse duk dai wannan dan bayani ya nuna mana yadda abubuwan suka faru haka. Wannan aiki ya binkito yadda tun asali mutumin Dutse baya daure wulakanci, amma ya yarda kuma yakan zama mai hakuri, juriya da dauriya wajen neman abin kansa ko kokarin ganin wani tsari ya tabbata matsawar yana kan gaskiya. Wani muhimmin abu da mai karatu zai lura dashi a cikin wannan dan bayani, watakil ya yi mamaki, shine tun asali mutumin Dutse ba ya dogaro ga wani a wajen neman wata bukata sai dai ya dage ya yi ta kokarin neman abu na kansa, sannan in ya samu ya rike da gaskiya kuma ya yi aikin da ake so. Ina fata wannan jawabi ya zama mai yin jagora ga fahimtar hakikanin Tarihin garin Dutse da Mutanensa. Don haka, ina rokon Allah ya sanyashi ya zama mai amfan ga kowa da kowa, Amin. |
|
|