|
|
|
TARIHIN RAYUWA DA AYYUKAN SARAKUNAN DUTSE Sarautar Tafara daga habe sannan Fulani suka karba kamar yadda aka ga a Kafuwa da Bunkasa Garin Dutse. rabon nasu ya kasance kamar haka
1.2 SARKI TSOHON MUTUM 1727-1797 AD 1.3 SARKIN DUTSE NATATA DAN TSOHON MUTUM 1797-1799AD. 1.4 SARKIN DUTSE GWAJABO DAN NATATA 1799-1807AD.
Tarihin kafuwar Dutse Kamar yadda aka gani a farko ya fara tun wajen 1450AD. Kuma mazaunan farko ba guri daya suka taru ba, sun zauna zama irin na gidan gona irin na gida can da can har zuwan wani Babarbare mai suna DUNA MAGU daya fara sawa Dutse suna DUTSE GADAWUR sakamakon wucewar wata GADA data wuce ta kusa dashi WUR dabai samu ya harbeta ba. Daga baya Habe mazauna farko suka taru gu daya a cikin GARU mazaunar MaSarautar Dutse ta yanzu. A wannan lokaci akayi wani shahararren Sarkin Dutse na Farko mai suna MAKURI wanda saboda shahararsa ya shiryawa Dutse tsaro har takai ya ginawa Dutse katangar gari data kewaye garuruwa wajen saba’in (70) da kofofi guda goma sha biyu (12) da akayiwa lakabi da inda aka yisu. Kofofin sune: - 1. Kofar Maranjuwa 2. Kofar Burtulan 3. Kofar yina 4. Kofar Kokiya 5. Kofar Bukka 6. Kofar Galadimawa 7. Kofar Ma’ai 8. Kofar Tago 9. Kofar Kaci 10. Kofar Gadadin 11. Kofar Galamawa 12. Kofar Rariya Saboda wannan shahara ta Sarkin Dutse MAKURI Sarkin Kano Kumbari ya turo mayakansa karkashin shugabancin wani shahararren mayakin bafullatani mai suna ADA a shekara ta 1732 dan a hana Sarkin Dutse MAKURI nufar Kano da yaki. Daga karshe su ADA sunci Dutse da yaki. Kuma ADA yayiwa Kano tawaye yaci gaba da Sarautar Dutse tsakanin 1732 – 1735, lokacin da aka kashe ADA. Kuma wani daga cikin shahararrun mayakan Dutse mai suna TSOHON MUTUM ya karbi mulki a matsayin sabon Sarkin Dutse daga cikin Habe. Kamar yadda za’aga zuri’ar Tsohon Mutum ita taci gaba da Sarautar Dutse a bangaren Habe har zuwa lokacin da Fulani sukazo a shekara ta 1807. 1.2 SARKI TSOHON MUTUM 1727-1797 ADMazauna farko sun zabi wani Habe BaKano mai suna Tsohon Mutum ashekara ta 1727 AD. Dan ya shugabancesu. Tsohan Mutum yayi shekara 60 (Sittin) yana Mulkin Dutse Gadawur a matsayin Sarkin Dutse. Watau 1727-1797AD. Wata rana ganin TSOHON MUTUM ya samu tsawon lokaci yana Mulki sai babbar matarsa sarauniya ‘yar Gyatum tace dashi “Anya kai kadai zakayi tayin Sarautane? Ga ‘yayan ka sun iso, ai sai ka basu kahuta. Sai yace da ita “Wallahi gaskiyarki”. wannan yasa yayi Murabus, ya nada dansa mai suna NATATA. a matsayin Sarki. Shikuwa tsohon Mutum ya koma gangaren Jigawa da zama. Wannan dalili yasa aka sawa wannan Unguwa “MARABUSAWA”. Acan Sarki Tsohon Mutum ya mutu aka binne shi a wani wuri yamma da inda ake kira Bariki ashekara ta 1797AD. Lokacin da tsohan Mutum yayi Sarauta ba a samu labarin wani yake-yake ba. Don haka babu wani abu da za’a bada labari yayi na gwanin ta wajen yaki. Sai dai zaman lafiya tsakaninsa da wadanda ya mulka watau ya Shugabanta. 1.3 SARKIN DUTSE NATATA DAN TSOHON MUTUM 1797-1799AD.Sarki Dutse Natata ba mutuwace tasa ya samu gadon Sarauta daga Mahaifinsa ba. Shi dadewa a mulki da tsawon shekarun Mahaifinsa yasa ya samu Mulki. Gashi kuma bai dade ba, Allah yayi masa rasuwa. Shi kam babu wani abu da za’a nunashi dashi wajen cin Nasara ko rashinta. 1.4 SARKIN DUTSE GWAJABO DAN NATATA 1799-1807AD.Wannan Sarki ya gaji Mahaifinsa Natata Kuma Sarkin Dutse Gwajabo shima bai dade ba, domin shekara 5 (Biyar) yayi yana Sarauta Allah ya karbi ransa 1799-1807AD. Sai dai shi Sarkin Dutse Gwajabo a lokacinsa Fulanin nan su biyu masu kamar ‘yan biyu salihi da Musa suka iso Dutse daga Borno wadanda kamar yadda za’aga a tarihim Sarautarsu. Sarkin Dutse Gwajabo yabar musu mulki don kashin kansa ya koma wata Unguwa da ake kira JIGAWAR SARKI. Yayi wa kansa murabus kuma ya mutu aka binneshi a can a cikin shekara ta 1807AD. Kafin mutuwar Sarki Gwajabo shi da Sarkin Dutse Salihi sun nuna tsari irin na ladabi da biyayya da suke nuna wa kansu wadda yajawo shi yayi wa kansa marabus wanda za a gani a tarihin Sarautar Fulani a gaba kadan. 2.1 SARKIN DUTSE NA DAYA (1) SALIHI DAN MALAM LAWAN (BAYILLIGE) 1807 – 1819AD. 2.2 SARKIN DUTSE NA BIYU (2) MUSA DAN MALAM AMADA 1819-1839 AD. (BAJALLIBE) 2.3 SARKIN DUTSE NA UKU (3) MUHAMMADU BELLO I 1840-1849AD. (BAJALLIBE) 2.4 SARKIN DUTSE NA HUDU (4) SARKI SULAIMANU I 1849-1868 AD. (BAJALLIBE) 2.5 SARKIN DUTSE NA BIYAR (5) IBRAHIM IREMA DAN SALIHI 1868-1884AD. 2.6 SARKIN DUTSE NA SHIDA (6) ABDULKADIR II DAN MUSA-MAJE ABALAGO 1884-1901AD. (BAJALLIBE) 2.7 SARKIN DUTSE NA BAKWAI (7) ABDULKADIR III DAN IBRAHIM 1901-1903 AD. 2.8 SARKIN DUTSE NA TAKWAS (8) HALIDU I DAN SULAIMANU I 1903-1910AD. (BAJALLIBE) 2.9 SARKIN DUTSE NA TARA (9) HALIDU II DAN BELLO I 1910-1911 AD. (BAJALLIBE) 2.10 SARKIN DUTSE NA GOMA (10) HAMIDA DAN IBRAHIM IREMA 1911 AD. (BAYALLIGE) 2.11 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA DAYA (11) ABDULLAHI DAN SULAIMANU I 1911-1916 AD. 2.12 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA BIYU (12) MAI UNGUWAR MUNDU BAWA AMADU GURARA 1916 –1917 AD. 2.13 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA UKU (13) BELLO II DAN ABDULKADIR I 1916-1922 AD. (BAYELLIGE) 2.14 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA HUDU (14) DAN LAWAN UMARU BAYOLE. 1922-1923 AD. 2.15 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA BIYAR 15 SULAIMANU DAN ALHAJI NUHU 1924 – 1960 (BAJALLIBE) 2.16 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA SHIDA (16) ALHAJI ABDULLAHI MAIKANO 1960-1983 AD. (BAJALLIBE) 2.17 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA BAKWAI (17) ALHAJI MUHAMMADU SANUSI DAN BELLO 1983-1995AD. (BAJALLIBE) 2.18 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA TAKWAS (18) ALHAJI NUHU MUHAMMADU SANUSI (BAJALLIBE) 1995 – DATE 2.1 SARKIN DUTSE NA DAYA (1) SALIHI DAN MALAM LAWAN (BAYILLIGE) 1807 – 1819AD. Sarkin Dutse Salihi shine Sarki na Farko a mulkin Fulani domin ya fara a shekara ta 1807 AD. Lokocin da Shehu Usman Dan Fodio ya fara jihadi a kasar Hausa. Bayan zamewar sa Sarki Salihi da abokin tafiyar sa Musa Sai suka yi shirin tafiya Kano dan Kai caffa wajen Sarkin Kano Sulaimanu. Da yake dama suna da halayyar yaki akan hanyar su ta zuwa Kano, sai da sukayi yaki da Dawakin Kudu suka kuma cinye Dawakin Kudu da wasu ‘yan garuruwa na kusa dasu kafin su shiga cikin Birnin Kano. Da suka shiga Kano Sarkin Kano Sulaimanu ya karbe su hannu bibbiyu har ma ya basu gida a inda mai burgami take a yanzu, wajan gidan Sarkin Dawakin tsakar gida. Kuma ya bawa Sarkin Dutse Salihi Rikon Unguwar sheshe, Darma, Zage Dantse da Gabari. Ana cikin wannan zama wata rana sai suka samu labarin ‘yan uwansu daga kasar Borno sun samu labarin suna zaune lafiya, kuma sunyi niyyar tahowa wurinsu. Jin wannan labari sai Sarki Salihi yaje wajen Sarkin Kano Sulaimanu ya sanar dashi niyyarsu ta komawa gida Dutse. Sarkin Kano Sulaimanu yace da Sarkin Dutse salihi “ayi haka? gashi muna zaune kamar uwa daya uba daya kuma wannan tafiya taku mai yiwuwa ta karya mana wannan zumunci”. Sarkin Dutse salihi yace, “Wannan zumunci namu in Allah yaso bamu rabuba muna tare”. Sai sukayi niyyar Komowa Dutse. Ya Kara da cewa yan uwansu da sukayi niyar zuwa wurinsu zasu zo da Dabbobinsu wadda a Dutse akwai ishasshiyar makiyaya. Domi nan Kano wata rana duk gari zata zama.Sarki Sulaimanu yayi na’am da wannan jawabi na Sarkin Dutse Salihi, su kuma suka kamo hanyar dawowa gida Dutse. Bayan sun Dawo Dutse sai Allah yayiwa Sarki Dutse Salihi rasuwa a shekara ta 1819AD. aka binne shi a cikin gidan Sarautar Dutse. Wannan ya nuna Sarki Salihi yayi shekara goma sha biyu kan gadan Sarautar Dutse. Wato 1807-1819 AD. 2.2 SARKIN DUTSE NA BIYU (2) MUSA DAN MALAM AMADA 1819-1839 AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Musa Dan Malam Amada ya zama Sarkin Dutse Bayan Mutuwar aminin sa Sarkin Dutse Salihi a shekara ta 1819 AD. Kafin ya zama Sarki, Musa dama ya manyanta kuma yayi shekara ashirin da daya (21) yana Sarauta. Saboda Tsufansa da kuma dadewa da yayi akan gadon Sarauta sai Sarkin Kano Dabo ya nemi Sarkin Dutse Musa Yayi Murabus. Kuma ya bada daya daga cikin ‘ya’yansa dan a nada shi Sarkin Dutse. Sarki Musa ya yarda yayi Murabus ya kuma bada dansa Chiroma Sulaimanu dan a nada shi Sarki. Amma Galadiman Kano Sani (ANGO) ya ki yarda a nada Chiroma Sulaimanu Sarkin Dutse, saboda a cikin ‘ya’yan Sarkin Dutse Musa akwai wanda yake auren ‘yar Galadiman Kano Sani, Kuma Galadima surikinsa Muhammadu Bello yake so a bawa Sarautar Sarkin Dutse. Dan haka Galadima ya aikowa Sarkin Dutse Musa ya aika da Barde Muhammadu Bello a nadashi, sai Sarkin Dutse Musa yace shi in baza a nada wanda ya bayar ba sai su nada wanda suka ga dama. Wannan yasa Sarki Kano Ibrahim Dabo ya umarci Galadiman Kano Sani (ANGO) ya kawo Muhammadu Bello (I) a nadashi yazama Sarkin Dutse na uku (3) a shekara ta 1840 AD. Wannan yasa Sarkin Dutse Musa yayi murabus yakoma “KATAGUM” da zama. Yana katagum ya samu labarin an kashe dansa Sarki Mohammed Bello (I) a Kano, kuma Sarki Kano na wannan lokaci Usman Maje Ringim ya sake aika masa da ya kawo dansa da ya fara Kawowa ayi masa Sarauta, watau Sulaimanu (I), shi kuwa ya bada sunnan Sulaimanu (I) aka nada shi Sarkin Dutse a shekara ta 1849. wannan yasa Sarkin Dutse Musa ya dawo Dutse daga katagum ya zauna a Murabus dinsa a Unguwar Fagoji inda ya mutu a shekara ta 1849 aka binne shi a Fagoji. kabarinsa yana nan Arewa da gidan Galadiman aska a Unguwar Fagoji. 2.3 SARKIN DUTSE NA UKU (3) MUHAMMADU BELLO I 1840-1849AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Mohammed Bello (I) na 3 a mulkin Fulani kafin nadinsa an sami Matsala Tsakanin MaSarautar Kano da Sarkin Dutse Musa Murabus. Wannan ya faru saboda tsarin biyayya da kokarin nuna gaskiya da Sarkin Dutse Musa yayi kokarin yi a lokacin da aka Umarceshi yayi Murabus saboda tsufa. Kuma ya kawo wani daga cikin yayansa a nada shi ya gajeshi. Aganin Sarkin Dutse Musa Murabus, Sulaimanu (I) yafi cancanta ya gajeshi kafin dan uwansa Muhammadu Bello I. Amma saboda tsari irin na Sarauta daga Kano, Galadiman Kano na wannan lokaci yana ganin ya kamata abawa Sirikin sa Sarautar ba wanda aka nemi Mahaifinsu Sarkin Dutse Musa Murabus ya bayar ba. Shi Sarkin Dutse Muhammadu Bello (I) Mutum ne jarimi na kwarai kuma mai Alheri gashi da kazamar kyauta. A zamanin sa Dutse ta shahara kwarai wajen samun Nasarar yake-yake, sai dai saboda wannan shahara tasa masu Mulkin Kano na wannan lokacin sai sukayi tunanin kar wata rana yazo yaci su da yaki. Sai suka tura a kirashi Kano suka kasheshi a shekara ta 1849. Bayan an kasheshi aka rike bayinsa, har yanzu wasu daga cikin ragowar bayin gidan Sarkin Kano asalinsu na Sarkin Dutse Mohammed Bello ne. Shi Mohammed Bello (I) shekara (9) tara yayi yana Sarautar Sarkin Dutse 1840-1849AD, Wanda ya karanta wannan tsari daga lokocin da aka umarci mahaifinsa yayi Murabus da yadda aka ki nada wanda yakeso a nada, mai karatu zai kara Fahimtar tsarin Sarauta da yadda take ko a yanzu, kuma in mutum yaga yadda bayan Muhammadu Bello (I) ya zama Sarki abin da ya faru tsakaninsa da wadanda suka nadashi da kuma yadda dan uwansa da aka ki ya zama Sarki da fari, wani yazo ya nadashi wannan zai karawa maikaratu da masu neman Sarauta Imani, tunanin komai na Allah ne, kuma komai kaddara ne kuma duk yadda Allah yaso tilas haka zai yiwu, dan haka in abu yafaru Mutane suyi hakuri da abinda Allah yayi Allah shi yabarwa kansa sani kuma komai da lokacinsa. 2.4 SARKIN DUTSE NA HUDU (4) SARKI SULAIMANU I 1849-1868 AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Sulaimanu I Sarki na 4 kafin yazama Sarkin wasu abubuwa sun faru da zasu karawa Mutane Imani. Domin lokacin da aka so yazama Sarki bai zamaba. kuma lokacin da yazama Sarki ya sharewa mahaifinsa hawaye Kafin Allah yayiwa mahaifin su Sarkin Dutse Musa rasuwa. Dama saboda halaiyarsa da kyautatawarsa da tsari irin nasa da Imani irin nasa tun farko sai yazama yashiga ran mahaifinsa. Kuma shine wanda mahaifinsa Sarkin Dutse Musa yayarda yayi murabus saboda yasan yana da magajin da zai kula dashi. Sarki Sulaimanu lokacin da yazama Sarkin Dutse ana wata rigina tsakanin MaSarautar Kano da ta Ningin Kasar Bauchi. Anyi yake-yake tsakanin Ningi da Kano kuma Ningawa sun yiwa kanawa barna mai yawan gaske domin sun kashewa kanawa manyan mutane da suka hada da Madakin Kano Ismaila da Makaman Kano Atiku. Azamanin mulkin Sarkin Dutse Sulaimanu I Hadejiyawa zamanin Sarkin Hadejia Buhari suka kawowa Dutse hari a lokacin wannan hari saida sukazo kofar garin Maranjuwa a inda Sarki buhari ya zauna agindin wata tsamiya abayan ganuwa. Da aka sami labarin zuwansu sai Chiroma Jaruma dan Sarkin Dutse Sulaimanu I yaje yatabbatar ya Komo ya sanarwa da mahaifinsa Sarkin Dutse Sulaimanu I wannan labari. Dajin haka sai Sarki Dutse Sulaimanu I yana karatun Dala’ilu ya tsaya da karatun dala’ilun ya bude bakin aljihunsa yace da Chiroma jaruma “Sai ka taho kashiga” Jin haka sai Chiroma jaruma ya juya ya zauna yayi alwala a shamakin Sarki ya fito daga gidan Sarki. Bai tsaya ko ina ba sai da yaje gaban karagar Sarkin Hadejia Buhari a inda yake zaune agindin tsaniya. Mutanen Sarki Buhari sun sami labarin abin da Chiroma Muhammadu Jaruma yayi wa Sarki Buhari gashi kuma Sarkin Hadejiya Buhari yayi alkawarin bazai kashe dan Sarkin Dutse Sulaimanu I ba. Kuma shi kadai yasan dalilin dayasa yayi wannan alkawarin. Wannan yasa Mutanen Hadejia sukaci gaba da saran ganuwar garin Dutse a kokarin su na shiga suci Dutse da yaki. A wannan kokari nasu saida sukayi amfani da wani abu da sukanyi na al,ada. Dama suna tafiya da wani Musaki duk sanda suke son suci gori da yaki. Sai su jefa shi kuturun takan katangar ganuwar garin da suka samu. Nan da nan sai su cinye gari da yaki. A Dutse da suka jefa wannan Musaki mai suna Badagari sai mutanen Dutse suka kasheshi sukayi gunduwa gunduwa dashi suka rinka jefowa mutanen Hadejiya shi takan ganuwa. Kuma ana harbi har aka sami Sarkin Hadejiya a hannu. Mutanan Hadejiya da ganin an harbi Sarki Bahari a hannu kuma an kashe Badagari sai Hadejiyawa suka bar Dutse suka bi arewacin Dutse- ganin Hadejiyawa sum bar Dutse sai Sarki Sulaimanu I yayi shirin tafiya yaki Ningi a shekara ta 1868AD. A wannan lokaci Sarkin Dutse Sulaimanu I yasa aka yanka “SA” ya tara yayansa yace marayu Kuzo ku karbi Naman karshe daga wajen mahaifinku. Kuma da yaga Dokinsa yana kartar kasa Kafin atafi Ningi. Sai Sarkin Dutse Sulaimanu I yace wa dokinsa “Bikili karya kakeyi ga gawar Barka gata Karensa” wannan Karin magana ta Sarki ta tabbata don kuwa an kashe Sarki Sulaimanu I da dokinsa bikili a fajewa a shekara ta 1868 shine dalilin da yasa ake ce masa maje Fajewa. Sarkin Dutse Sulaimanu I ya yi shekara goma sha tara (19)yana Sarauta. 1849-1868. Sarautar Sarkin Dutse Sulaimanu I ta numa mana abubuwa guda uku 3. 1. Sarki tun farko mai biyayayane ga iyayensa. 2. Mahaifinsa Musa yanuna wa jamma’a cewa lallai dan Adam yayi dogaro ga Allah. 3. Yarda da Allah takan sa muturn yasami masara. 2.5 SARKIN DUTSE NA BIYAR (5) IBRAHIM IREMA DAN SALIHI 1868-1884AD. Sarkin Dutse Ibrahim Irema yazama Sarkin Dutse na 8 a tsarin Sarauta Dutse gaba daya, Sarkin Dutse na 5 biyar abangaren Sarautar fulani kuma Sarkin Dutse na 2 a bangaren yalligawa (Gidan Salihi) domin shine Sarki na farko da ya gaji Sarkin Dutse Salihi. Saboda da Sarki Salihi da ya mutu abokinsa Musa ne yagajeshi. Yazama Sarkin Dutse na farko a fangaren jallibawa. Da Sarkin Dutse Sulaimanu I maje Fajewa yarasu a fajewa an sami canjin Sarki a Kano, Sarkin Kano a wannan lokaci shine Sarkin Kano Abdullahi maje karofi. Kuma shi ya nada Sarki Ibrahim Irema Sarkin Dutse. Sarkin Dutse Ibrhim Irema azamaninsa ba’ayi wasu muhimman yake-yakeba wannan yasa ya fara da rigimar yau uwa. Dahawansa Sarauta sai ya umarci yan uwansa ‘ya’yan Sarkin Dutse Sulaimanu I subar masa kasarsa saboda basuyi masa mubayi’aba. Wadannan yan uwa nasa su Chiroma Muhammadu Jaruma. Makama Musa, Barwa Amadu da Dan iya Hammawabe suka tafi Kano suka yi kara agaban Sarkin Kano. Sarki Kano ya aiko a tambayi Sarki Dutse abin da yahadasu har haka tafaru. Sarkin Dutse Ibrahim Irema ya aikawa da Sarkin Kano Abdullahi maje Karofi da cewa sudai Mutane ne marassa san zaman lafiya. Kuma wasu masu haddasa fitina da rashin zaman lafiya suke zugasu suyi gaba dashi. Wannan yasa Sarkin Kano Abdullahi Maje karofi ya’aiko agayawa Sarkin Dutse Ibrahim Irema cewa bazasu bar Dutse ba. Kuma su zauna lafiya da junansu. Wannan yasa Sarki Dutse Ibrahim Irema yace to amma badai su zauna inuwa daya dasu ba. Wannan yasa akayi musu gidaje a Unguwar katangare daidai tsohon asibitin kutare nan akayiwa Madaki Abubakar Gida kudu dashi akayi wa dan ‘iya Hammawabi gida. Shikuma Chiroma Jaruma ance makaru aka yimasa ya tafi ya mutu agona. Ganin yadda Sarkin Dutse yayi musu sauran yayan Sarki Sulaimanu I sukace sun barwa Allah ya saka musu. Bayan wadannan abubuwa sun faru shikuma Sarkin Kano Abdullahi maje Karofi ya rasu. Dan uwansa Muhammadu Bello yagajeshi. Yazama Sarkin Kano dafara wannan fada sai fadawa suka fara saran Sarki Dutse Ibrahim Irema agun sabon Sarkin Kano Muhammadu Bello. Jafa’in da jakadan da aka turo ya tafi da Sarkin Dutse Ibrahim yayi masa shine wai Sarkin Dutse Ibrahim Irema ya debi yan mata 70 samari 70 ya ajiye agidansa. Sarkin Kano Muhammadu Bello ya turo aka tafi da Sarkin Dutse Ibrahim Irema Kano. Dayaje ya tambayeshi shin wannan magana haka take? Sarkin Dutse a fusace ya amsa wa Sarki Kano cewa “wannan ko Fira’una aiba zaiyi wannan karyaba”. Yayi wo waje. Wannan yasa Sarkin Kano Muhammadu Bello yasa akaishi soron ajiya. Shi wannan soron ajiya wurine da akayi Imanin in an kai mutun cikinsa sai wani bashiba. Domin can aka kai Sarkin Dutse Bello kuma a can ya mutu. Da yamma tayi aka tura aga halin da Sarki Dutse Ibrahim Irema yake ciki ko ya mutu sai aka sameshi a zaune daram yana jan Carbinsa. Kuma gashi har an bada Sarautar Dutse ga wani dan uwan Sarki Ibrahim. Sarkin Kano Muhammadu Bello yasa aka fito dashi ya kuma gaya masa gashi har an nada Sarkin Dutse. Sarki Ibrahim yatambaya wa aka nada? akace dashi kaninka Abdulkadir I aka nada. Sai yace amma kanawa kun cucemu inama awani kini akayiwa da sai anyi tara watakila na goman yayiwu. Amma bakomai. Sarkin Kano Muhammadu. Bello ya bawa Sarkin Dutse Ibrahim hakuri ya kuma gaya masa duk abin da yasa wannan abu yafaru haka. Ya kuma gaya masa maganganun fadawa da duk abin da jakadan da aka turo shi gunsa yazo fadar Kano ya fada. Dan haka yanemi Sarki Ibrahim yayi masa gafara.yakuma gayawa Sarkin Dutse Ibrahim gashi kuma an nada sabon Sarkin Dutse dan uwanka, kaninka Abdulkadir. Sarkin Dutse Ibrahim yace da Sarkin Kano Muhammadu. Bello “To iyalaina sunyi kukan hawaye amma na wani sai sunyi hawayen jini.” Sarkin Kano Muhammadu Bello ya kara bashi hakuri. Kuma yace yabawa Sarkin Dutse Ibrahim Irema “wurma ya kuma halarta masa Harajinta. Daga baya aka fahimci ashe limamin Dutse Yamusa ne yayi niyar tafiya makka aikin Hajji. Wanda Sarkin ya turo a tafi dashi da duk wadanda sukayi niyyar tafiya tare dashi da ba’a sameshi ba. Kuma da rigimar da ta shiga tsa kaninsa da mutan fada aka kulla wannan zance na cewa Sarki ya sami yara yan mata 70 da yara maza 70 ya ajiye su a gidansa. Bayan gaskiyar magana tafito gashi kuma an riga anyi hukunci Sarkin Kano ya kara bashi hakuri. Kuma bayan nan wasu dalilai irin na mulki suka taso Sarki Ibrahim yana Wurma aka tube shi acikin shekara to 1884AD. yayi Hijra zuwa Hadejia. Ya mutu a Hadejia acikin shekarar 1884AD. 2.6 SARKIN DUTSE NA SHIDA (6) ABDULKADIR II DAN MUSA-MAJE ABALAGO 1884-1901AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Abdulkadir II yazama Sarkin Dutse ashekara ta 1894AD. lokacin da Sarkin Kano Aliyu yazama Sarki. Bayan sun kori Sarkin Kano muhammadu Tukur. Bayan nada Sarkin Dutse Abdulkadir II Sarki sai yaki tsakanin Dutse da Hadejiyawa yadawo a cikin shekara ta 1901AD. Hadejiyawa sai da suka zo har shatari da yaki. Dalilin wannan yaki ance wai Hadejiyawa suna kan hanyarsu ta Kano saboda kurum wai akwai kyakkyawar jituwa tsakanin Kano da Gumel abokiyar gabarsu. Hadejiyawa sun kashe Sarkin Dutse Abdulkadir II dan Musa ashekara ta 1901AD. An dauko gawarsa zuwa Abalago inda aka binneta, shi yasa ake cewa dashi Sarkin Dutse Abdulkadir Maje Abalago. Kuma yayi shekara 7 bakwai yana Sarauta. Kuma shine na uku a zuriyar Musa da ya rasu a yaki. 2.7 SARKIN DUTSE NA BAKWAI (7) ABDULKADIR III DAN IBRAHIM 1901-1903 AD. Sarkin Dutse Abdulkadir III dan Ibrahim yazama Sarkin Dutse bayan mutuwar Sarkin Dutse Abdulkadir II. Sarkin Dutse Abdulkadir III ana yimasa lakabi da DamaMusau. A bayanda yazama Sarki Abduklkadir III damaMusau ya bi Sarkin Kano Aliyu ya raka shi su kai caffa wajen Sarkin musulmi Attahiru a sokoto. Kuma bayan sum bar Kano sai turawa sukaci Kano da yaki. Akan hanyarsu ta dawowa sun kafsa da sojojin turawa a Kotorkoshi. Abdulkadir yayi yaki sosai amma ba a kasheshiba a karo na farko. Kuma wannan yakara masa karfin gwuiwa ya bi Sarki Attahiru nanma anyi yaki amma baa kashe Dama Musauba. Wannan yasa yayi zamansa bai dawo Dutse ba ya zauna tare da Sarkin musulmi attahiru. Yarasu ashekara ta 1903 AD. 2.8 SARKIN DUTSE NA TAKWAS (8) HALIDU I DAN SULAIMANU I 1903-1910AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Halidu dan Sulaimanu I Sarkin Kano Abbas wanda Turawa suka nadashi shine yanada shi Sarkin Dutse a shekara ta 1903AD. A wannan lokaci ashekara ta 1908AD wani Bature Residan na Kano Dr. cargill. Ya sakewa Dutse fasalin taswira ya fidda Harbo kila da yarfi da Kiyawa wadda itama da take cin gashin kanta. Sarkin Dutse Halidu yana daga cikin Sarakunan da mulkin Turawa ya sauke domin sakaci. kuma shi da aka tube shi ya koma Unguwar Yakasai cikin birnin Kano dazama. Yamutu a yakasai aka binne shi a Kano a shekara ta 1910.AD. 2.9 SARKIN DUTSE NA TARA (9) HALIDU II DAN BELLO I 1910-1911 AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Halidu Dan Bello I ya zama Sarkin Dutse a Shekara ta 1910 bai dadeba domin yayi shekara daya da wata goma (10) aSarauta akatubeshi. Sarki halidu dan Bello da aka tubeshi ya dawo wata Unguwa da ake kira Burtulan garin mahaifiyarsa yarasu acan ashekara ta 1911 AD. 2.10 SARKIN DUTSE NA GOMA (10) HAMIDA DAN IBRAHIM IREMA 1911 AD. (BAYALLIGE) Sarkin Dutse hamidan dan Ibrahim Irema Sarkin Kano Muhammadu Abbas ne ya nadashi yazama Sarkin Dutse na Goma sha biyu (12). Allahu akbar wannan Sarki kwanan sa biyar (5) aSarauta Allah yayi masa rasuwa kafin yadawo Dutse kuma anbinne shi a Kano ashekara 1911 AD. Kuma a zuriyar Salihi shine Sarki na uku kuma na sha biyu a Sarautar Fulani. 2.11 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA DAYA (11) ABDULLAHI DAN SULAIMANU I 1911-1916 AD. Bayan rasuwar Hamida dan Ibrahim sai Sarkin Kano Abbas ya nada Abdullahi I dan Sulaimanu I ya zama Sarkin Dutse ashekara ta 1911 AD. wannan Sarkin ya zauna a chimada kafin akirashi zuwa Kano don a tubeshi ashekara ta 1916AD. Kafin yazo Kano Sarkin Kano Abbas ya Baiwa mai Unguwar Mundubawa Amadu Gurara Mukamin Hakimin Dutse. 2.12 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA BIYU (12) MAI UNGUWAR MUNDU BAWA AMADU GURARA 1916 –1917 AD. Bayan tube Sarkin Dutse Abdullahi, Sarkin Kano Abbas ya baiwa Mai Unguwar Mundubawa Gurara Sarautar Hakimin Dutse a shakara ta 1916AD. Wannan sabon Hakimi kafin yazo Dutse ya turo aka tafi masa da Bello dan Abdulkadir I dan Salihi zuwa Kano. Dazuwansa Kano Sarkin Kano Abbas ya nada shi a mukamin Hakimi kuma aka bashi Limawa, Kachi da Gurin Galamawa. Kuma Sarkin Dutse Bello II da sauran Digatan suka zauna karkashin sabon Hakimin su. Mai Unguwar Mundubawa Amadu Gurara ya tara kudin jangali da ba’a taba tara kamarsa ba. Ganin wannan kokari na mai Unguwar Mundubawa sai DIO na wannan lokaci ya bawa Sarkin Kano Abbas dama da ya duba, bawa mai Unguwar Mundubawa wata babbar Sarauta. Wannan yasa Sarkin Kano ya canja masa Sarauta ya zama Dan-Lawan. An cireshi daga Sarauta a shekara ta 1917AD. akan laifin barnatar da kudin Jama’a. Shigowar wadansu Fulani Sarautar Dutse ya biyo gazawar fulanin Dutse dayawan ciresu da akeyi bisa lai fukan da basu taka kara sun karyaba. Wannan aganin Sarakunan Kano ya nuna Fulanin Dutse sun yasar da damarsu shi yasa suka nada wani ba daga cikin mutanen Dutse ba. Haka tsarin Sarautar yake kokuma ince haka tsarin mulki yake agun wanda yake kan gado. Wani yayi dai dai wani yayi kishiyar haka. 2.13 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA UKU (13) BELLO II DAN ABDULKADIR I 1916-1922 AD. (BAYELLIGE) Sarkin Dutse Bello II Dan Abdulkadir da a ke yiwa lakabi da Maje Katanga ya zama Sarkin Dutse ashekara ta 1916AD. Shima bai dade ba. Domin shekararsa shida aka tubeshi ya koma Katanga a matsayin Murabas. Yarasu a Katanga a shekera ta 1922AD. 2.14 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA HUDU (14) DAN LAWAN UMARU BAYOLE. 1922-1923 AD. Nadin Sarkin Dutse Dan Lawan Umaru Bayole yasa aka raba kasar Dutse gida biyu, Dutse da kiyawa. DanLawan umar ya koma Kiyawa har zuwa 1932. Dan Lawan Umar an kaishi Kiru kuma aka sake hade Dutse da Kiyawa a karkashin Mulkin Sarki daya a 1932 AD. 2.15 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA BIYAR 15 SULAIMANU DAN ALHAJI NUHU 1924 – 1960 (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Sulaimanu II dan Alhaji Nuhu kafin nadin sa Sarki a shekara ta 1924 Sarkin Kano Usman Na II Maje Shekara, ya turoshi Dutse a shekara ta 1923 don ya zauna tare da Sarkin Dutse Dan Lawan Umaru kafina a yanke shawara. A cikin 1924AD. Aka yanke shawara D.O. Mr. Nor, yazo Dutse yanada Alhaji Sulaimanu II a matsayin Sarkin Dutse. D.O yaturo akira Sarkin Dutse Dan Lawan Umaru da Sulaimanu II dan Alhaji Nuhu su sameshi a Andaza. Da sukazo Andaza suka sameshi, sai ya sanar dasu an raba Dutse gida biyu, Dutse Yamma Da Dutse Gabas. Dutse yamma an bata Digatai 35 kuma an nada AlhajiSulaimanu II yazama Sarkinta kuma ya zauna a Dutse. Dutse Gabas kuma aka bata digatai 25 aka umarci Dan Lawan Umaru ya zama Hakimin Kiyawa kuma an umarceshi daya koma Kiyawa da zama. Yawan Digatan kasar Dutse lokacin Sarkin Kano Abbas watau lokacin dan Lawan Umaru yana Sarkin Dutse Digatai Ashirin da Takwas (28) ne. 1. ANDAZA 2. ABALAGO 3. CHAMO 4. CHIROMAWA 5. DUTSINBUJI 6. DURU 7. DAGWAJE 8. FAKE 9. GURUN GALAMAWA 10. KWANDA 11. KIYAWA 12. KATANGA 13. KARGO 14. KUDAI 15. KARFAWA 16. KACHI 17. KATUKA 18. LIMAWA 19. MADOBI 20. MAJE 21. RURU 22. SAKWAYA 23. TSURMA 24. WARWADE 25. WANGARA 26. WURMA 27. YALWA 28. YARGABA Kuma a lokacin Dan Lawan Umaru aka sakewa Garuruwan Digatai tsari aka ciri wasu daga jikin wasu aka tada wasu. Suka zama Digatai Hamsin da Bakwai (57) kamar haka. 1. ANDAZA 2. ABALAGO 3. AKAR 4. ABAYA 5. BUJU 6. CHAMO 7. CHAI-CHAI 8. DURU 9. DUNDUBUS 10. DAGWAJE 11. DANTAWUYA 12. DUHUWA 13. DAN FUSAN 14. DUNGU 15. DARA’U 16. FANISAU 17. FAKE 18. FIYA 19. GURDUBA 20. GURUM GALAWAWA 21. GURUM BAYANGARI 22. HADDORI 23. ISARI 24. JIDAWA 25. JAUDI 26. JIGAWAR TSADA 27. KACHI 28. KARGO 29. KUDAI 30. KWADIYA 31. KWAIMAWA 32. KWANDA 33. KATUKA 34. KIYAWA 35. KARNAYA 36. KYARAN 37. KARFAWA 38. KATANGA 39. KUMI 40. KACHA 41. LIMAWA 42. MAJE 43. MAZAZZAGA 44. MALAMAWA 45. MADOBI 46. RURU 47. SABON GARI 48. SAKWAYA 49. TUNANNAN 50. TABOBO 51. TURHO 52. TSURMA 53. WARWADE 54. WURMA 55. WANGARA 56. YARGABA 57. YALWA Suma da akazo rabon su an kara digatai guda uku suka zama Digatai Sittin (60). Ga yadda akayi rabon. GUNDUMAR DUTSE 35. ABAYA 36. BUJU 37. CHAMO 38. CHAICHAI 39. DUNDUBUS 40. DURU 41. DARAU 42. DAGWAJE 43. DANTAUYA 44. FANISAU 45. GAKMAWA 46. GURDUBA 47. ISARI 48. JIDAWA 49. JAUDI 50. JIGAWAR TSADA 51. KACHI 52. KARGO 53. KUDAI 54. KWADIYA 55. KACHA 56. KARNAYA 57. KYARAN 58. KWAIMAWA 59. LIMAWA 60. MALAMAWA 61. MADOBI 62. RURU 63. SAKWAYA 64. TABOBO 65. WARWADE 66. WURMA 67. WANGARA 68. YARGABA 69. YALWA DIGATAN GUNDUMAR KIYAWA1. ABALAGO 2. AKAR 3. ANDAZA 4. DUHUWA 5. DAN FUSAN 6. DAN TAWUYA 7. DUNGU 8. GARKO 9. GARUN BAYAN GARI 10. GORUMO 11. FANISAU 12. FAKE 13. HADDORI 14. KYAWA 15. KARFAWA 16. KANGA 17. KATUKA 18. KWAUDA 19. KUMI 20. MAJE 21. MARAZZAGA 22. SABAN GARI 23. TURHO 24. TSURMA 25. TUNANNAN. Wata kila mai Karatu yayi mamakin ganin Mutamen Dutse sunje sun yi Sarauta a Gwarzo kuma Mutanen Kano misali su Mai Unguwar Mundubawa Amadu Gurara da Dan Lawan Umaru sunzo sun Mulki Dutse. Wadannan tsare-tsare ne irin na Turawa da canjin zamanin da Sarauta ta samu kanta a ciki. Kafin nadin Sarkin Dutse Sulaimanu II za’aga an nado Sarki daga Kano a matsayin digacin Limawa, Kachi da Gurum Galamawa. aka kuma sake nado Sarkin Limawa Abubakar dan Sarkin Dutse Ibrahim Irema Dan Salihi a matsayin Hakimin da ya canji Dan Lawan Umaru Gurara. shi kuma dan Lawan aka tubeshi a shekara ta 1924AD. Mutanen Dutse daga zuriyar Sarkin Dutse Musa da sukayi Sarauta a Gwarzo a matsayi Sarkin Dawaki Mai- tuta sune: - 1. Sarkin Dawaki na Ta’ala Hakimin Gwarzo 1916-1942. AD. 2. Sarkin Dawaki Mai-tuta Abubakar Hakimin Gwarzo 1942- 1950.AD. 3. Sarkin Dawaki Mai-tuta Mahammadu Inuwa Hakimin Gwarzo1950-1952.AD. 4. Daga karshe Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya nada Mutumin Dutse Alhaji Sarki Sulaimanu ya zama Hakimin Gwarzo a mukamin Durbin Kano 1983-1994AD. Sarkin Dutse Sulaimanu II saboda kwazo irin nasa yasa aka sake hade Dutse da Kiyawa a 1921 suka koma gunduma daya yaci gaba da mulkinsu amatsayin kasa daya watau gundumar Dutse. Saboda su Turawa suna kula da abin da Ma’aikatansu sukeyi dazarar Mutum yayi wani abu na kirki sai a saka masa da wani aku na Alheri haka kuma in mutum yayi rashin kirki sai a horeshi. Sarkin Dutse Sulaimanu II zamewarsa Malamin Makaranta dazuwansa sai yasa himma ga bumkasa Ilmi. Lokacinsa “Ya”yan wannan kasa ta Dutse suka shiga Makarantar Boko daban-daban Ajihohin Arewa. kuma wasu daga cikinsu suka samu tafiya Makarantu Akasashen Turai don karo Ilmin a fanni daban-dabarn. Alokacin wannan Sarki, Dutse ta samu cigaba a wajen ginin Makarantu. 1. Angina Makarantar Elementary ta farko a Dutse a shekara ta 1936AD. 2. Angina Makaratar Elementary ta biyu a Kiyawa a shekara ta 1949AD. Sarkin Dutse Sulaimanu II shi yake daukar nauyin duk wanda yasamu tafiya Makarantar Medil ta Kano ga wadanda iyayensu bazasu iyaba. 3. A lokacin Sarkin Dutse Sulaimanu II aka gina Makarantar “Medil” (Senior Primary School Takur) a takur a 1960. 4. A lokacinsa aka yi wadansu Hanyoyi da suka hada garuruwan Dutse. 5. A Lokacinsa aka gina asibitoci a Dutse da Kiyawa. 6. A lokacinsa aka gina Rijiyoyin kankare suka samu kyakkyawan Ruwan sha aka samu saukin ciwace-ciwace irinsu Kurkunu. 7. Wani babban abu shine saboda kwarewarsa wajen mulki Sarkin Dutse Sulaimanu II shi MaSarautar Kano take bawa wakilcin madakin Kano duk sanda Madakin Kano yayi tafiya. 8. Wannan kwarewa ta Sarkin Dutse Sulaimanu II tasa aka bashi lambar girma ta M.B.E. ranar 31 ga watan mayu 1956AD. Kuma Allah ya bashi Ilmin Arabiyya don haka ya taimaka kwarai wajen daukaka Addinin Muslinci, ta wajen gina masallatai da kokarin ganin Malamai sun hada kawunansu. Saboda kokarinsa na hada kan kasa Sarkin Dutse Sulaimanu II a shekara yakan tsara ran gadin kasarsa don yayiwa Jama’a kaliye don a zauna Lafiya. A irin wannan rangadine yadawo daga Warwade da matsanancin ciwon gudawa ranar 15 ga watan Yuni 1960AD. An kaishi asibitin Kano ranar 21 ga watan Yuli 1960AD. Allah yayi masa Rasuwa a Kano ranar Juma’a 22 ga watan yuli 1960AD. Aka binneshi a Gwale ta Kano. Sarkin Sulaimanu II dan Alhaji Nuhu ya shekara Talatin da shida (36) yana Sarauta 1924-1960AD. 2.16 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA SHIDA (16) ALHAJI ABDULLAHI MAIKANO 1960-1983 AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano Shine Babban dan Sarkin Dutse Sulaimanu II, Wanda ya rasu ranar Juma’a 22 ga watan yuli 1960AD. Kafin ya zama Sarkin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano yayi aiyuka iri-iri karkashin Kano N.A. (Karamar Hukumar Kano) yayi aikin Malamin Hakimi a Bichi, Yayi Aikin Haraji a Kano, Yayi wakilin Asibiti a Kano wadannan aiyuka sunsa ya sami goguwa ta Rayuwar aiki da zaman sa na Duniya kafin ya shiga harkokin Siyasa. Alhaji Abdullahi Maikano ya shiga harkokin Siyasa a shekara ta 1949 kuma ya zama Shugaban Jam’iyyar NPC “Jam’iyyar Mutanen Arewa” reshen yankin Kano (Kano Province) a shehara ta 1956. Bayan yayi shugabancin NPC likkafa tayi gaba Alhaji Maikano ya zama Ministan Kananan Hukumomi na jihar Arewa watau N.A. N.A. daga shekara ta 1957 zuwa 1960AD. karkashin Shugabancin Alhaji Sir. Amadu Bello Sardaunan Sokoto Primiyan Jihar Arewa na Farko. Alhaji Abdullahi Maikano yana Minista Mahaifinsa Sarkin Dutse Sulaimanu II ya rasu, kuma Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi yanada Minista Alhaji Abdullahi Maikano Sarkin Dutse ranar Litinin 15 ga watan Augusta 1960AD. Sarkin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano mutum ne mai Hakuri, Dauriya kuma mai kokarin bin umarnin nagaba dashi. Wannan yasa yasami gogaiyar aiki da Jama’ar Nigeria iri daban daban daya samu kansa tare dasu. Kuma Sarkin Dutse Abdullahi Mutum ne mai saukin kai da Hikima halayan da sukasa ya zauna lafiya da Shugabanninsa da Jama’arsa. Sarkin Dutse Abdullahi Maikano ya fara Sarauta lokacin Sarauta tana da Martaba da yawan gaske. Domin in an duba Mutum yabar Minista yadawo ya zama Hakimi lallai wannan abu ba karami bane. Da za’a kwatanta da wannan lokaci mutum ko Darekta yakeyi aka bashi Hakimi mai Kasa baya barin Darektannan ya dawo ya zauna ga aikin Hakimci. Sai dai yayi Wakili ya zauna masa tare da Jama’arsa shi kuma ya rinka zuwa kasarsa a lokaci-lokaci. A nan nema nake ganin yakamata nabada shawara kan lallai Hukuma da majalissun Sarakuna su dubi wannan tsari indai mutum ya karbi Hakimi mai kasa yabar aikin Gwamnati ya koma ya zauna tare da Jama’arsa. A wannan lokaci na Hakimin Dutse Sarkin Dutse Abdullahi Maikano ya zama mai cikakkiyar biyayya ga MaSarautar Kano da shugabancin Gundumar Birnin Kudu. Halayan da suka sa yasamu biyan bukatunsa yayin da ya tashi nemawa Jama’arsa abubuwa daga wajen Hukuma. A bangaren Ilmi an samu cigaba dayawa domin acikin (1960) yayi kokarin ganin an samu Makarantar Medil watau Makarantar gaba da Firamare wadda aka tsara daukar yaran ELimantare ta Dutse da Kiyawa don suyi Ilminsu na gaba da Firamare. Wannan Makaranta ta fara a cikin Garu da yara Arbain (40) karkashin shugabancin Mallam Shehu Gezawa. Daga wannan lokaci aka cigaba da samun Karin Makarantu suka tashi daga Biyu (2) zuwa Goma Shabiyu (12) wato tsakanin 1960-1972AD. Sarkin Dutse yana cikin aiki tsarin Ilmi bai daya (UPE) na kasa da ya shigo a 1976AD. Makarantu suka koma 194. Wannan tsarin na Ilmi bai daya ya shigo kuma an samu sabon tsarin mulkin kananan Hukumomi na 1976AD. da ake yiwa lakabi da Sabon Tsarin Kananan Hukumomi Na Dasuki. Domin dasukine ya shugabanci wannan kwamati da yayi wannan aikin. A shirin sabon wannan tsarin Dutse ta samu karamar Hukuma watau Dutse ta zama karamar Hukuma watau Dutse L.G.A. dama anga takaitaccen jawabi kan wannan tsari abaya. Sarkin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano kamar dukkan Sarakuna wannan tsari yazo masa ba yadda aka zata ba. Domin awannan tsari Gwamnati ta kawo wakilinta a matsayin wakilan riko. Hukumar tanada Shugaba watau “Chairman”da kawunsilolinsa domin su aiwatarwa da Gwamnati manufarta. Dokar kasa ta tabbatar da kafa kwamitocin riko ga dukkan sabbin kananan Hukumomi a Nigeria. A Dutse Alhaji Abubakar Bello Dutse shi ya shugabanci Kwamitin rikon wanda Alhaji Bello Da’u yayiwa Sakatare. Wannan Kwamiti shi ya rike karamar Hukumar Dutse har akayi zabe. Wadanda aka zaba dai an zabesu amma Gwamnati ce ta nada musu Shugaba ragowar suka zauna a matsayin Kansiloli, Zababbun yan majalissar sune: - 1. Alhaji Basiru Dutse Shugaba 2. Alhaji faruk Ahmad Wangara Wakili 3. Alhaji Buba Sulaiman Katanga Wakili 4. Alhaji Musa Sakwaya Wakili 5. Alhaji Ibrahim Nakarofi Wakili 6. Alhaji Bello Da’u Sakatare Yadin Dutse ko ince Fagoji shine yazama mazaunin karamar Hukumar. Zamewar wannan wuri sabon mazauninta, karamar Hukumar ta fara da gina Sakatariyarta da gidajen manyan Ma’aikata. A gaskiya wannan karamar Hukuma ta cancanci yabo saboda irin ayyukan datayi wadda Jihar Jigawa ma da’akayi da wadannan gidaje akayi amfani wajen mazaunin sabuwar Jihar da akayi a 1991AD. Wajen jin dadin Jama’a wannan karamar Hukuma ta gina Rijiyoyin Kankare, kananan Hanyoyi da suka hada manyan garuruwan da suka hada Karamar Hukumar da Dutse, Cibiyar Karamar Hukumar, Asibitoci da gina sabbi da gyaran Makarantun Firamare saboda aiwatar da sabon tsarin Ilmi na kasa UPE domin duk an dawo da wadannan ayyukan karkashin Kananan Hukumomin. MATSAYIN HAKIMAI A SABBIN KANANAN HUKUMOMI Hakimai sun zama masu bada shawara a wannan tsari domin kamar yadda aka nuna abaya canjine yazo. A wani lokacima ko tuntubarsu ba’ayi sai dai suga ana aiwatar da ayyuka. Irin wadannnan abubuwa na maimaita basu yiwa Sarakuna da Hakimansu dadiba. Wani abu na rashin dadi da ya faru anan Dutse shine maganar ginin sabon Masallacin Juma’a a garin Sabon Garin Danmasara Unguwa a kasar Dagacin Kargo. Dama haka Tarihi yake a karanta wani gun aji dadi wani kuma aji rashinsa. Amma dalilin haka shine acigaba a inda akaji dadi kuma a gyara kuskuren inda aka bata. Maganar Masallacin Juma’a, karfin mulki da karfin iko sun taso tsakanin Sarkin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano da Alhaji Basiru Dutse Shugaban Karamar Hukuma daya bada izinin a gina Masallaci a Sabongarin Dan Masara ya kuma je ya bude batare da sanarwa da hakimin Dutse ba. Wannan ya jawo rubuce rubuce tsakanin ofishin Hakimi da MaSarautar Kano zuwa karamar Hukuma. Hakika wannan sha’ani baiyi kyauba kuma shi yazama sanadin karfafa wata gaba data faru a nan Dutse. Za’aga yadda abin yakasance a gaba kadan. Abiyo Tarihi. Sarkin Dutse bai goyi bayan bude wannan masallacin Juma’a ba saboda karkashin tsarin Sarauta yake. Domin kamar yadda yace. Kafin agina masallacin Juma’a sai Sarki ya sani kuma ya kayi mutanen gaban Sarkin Kano anyi musu tambayoyi. Kuma in an gama za’a bude sai an kayi wadanda ake gani su zasu zama Liman da Na’ibi anyi musu tanbayoyi domin aga kwarewarsu in sunci jarrabawa Sarki ya bada izini a nadasu suzo suci gaba da Sallah a sabon masallaci. Ganin faruwar wannan tsari sai Sarkin Dutse ya rubutawa ofishin Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero domin susan halin da ake ciki. Ga yadda rubuce rubucen suka kasance. Wasika daga ofishin Hakimin Dutse: -
24/4/1978. Zuwa ga, Mai-Girma Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayaro.
GINAWA DA BUDE MASALLACIN JUMA`A, DA NADA LIMAMI, DA NA`IBI DA YIN IZININ FARA SALLAH A UNGUWAR SABON GARIN DANMASARA TA KASAR DAGACIN KARGO, BA TARE DA IZININ MAI-GIRMA SARKIN KANO BA. Bayan gaisuwa da girmamawa maiyawa, sanarwa da Mai-girma Sarkin Kano Allah ya taimakeshi, Amin. A ranar 6/4/1977, na sami takarda daga wani Mallami mai duba aikin gayya na karamar hukumar Dutse da Jahun, mai suna Mallam Abdu Muhammadu wanda a cikin takardarsa ya baiyana mani cewa mutanen Unguwar Sabon gari Danmasara sun bashi sha`awar da suke da ita ta gina Masallacin Juma`a babba, harma yace dani yaga dagacinsu na Kargo marigayi Alhaji Inusa ya shaida masa, akan wannan al’amari, inda shi Digacin kargo ya tabbatarwa wannan Malami gaskiyar wannan al’amari cewa shine yayi hakane, harma sun tara kudi masu yawan gaske, batareda sani na ba, inji shi Digacin kargo mai mutuwa Alhaji Inusa. Akan wannan sai shi Mallam Abdu Muhammadu, Malamin duba aikin gayya yarubuto mani (Hakimin Dutse), takarda wannan labari, ta ran 6/ 4/ 1977AD. Bayan kwanaki biyu da samun wannan takarda ta Mallam Abdu Mahammadu sai gashi mutanen wannan Unguwa bisa jagorancin Mallam Isa Usman kimanin su 5 ko 7 sunzu gareni don neman izinin su tara kudi, kuma su gina Masallacin Juma’a kuma su cigaba da yin SAllah aciki. To dajin haka sai naja hankalinsu game da Umarnin Mai-girma Sarkin Kano, wanda Madakin kano, ya aika ga dukkan Hakiman Kano, akan takarda mai lamba PUB/ II/ 331 ta ran 21st October, 1975AD. Da takarda ta biyu mailamba PUB/ II/ V/ 385 ta ran 26th October, 1976AD. Wadda acikin wadanan takardu akayi mana bayanin ka’idojin ginin Masallacin Juma’a, kuma aka gargademu da cewa kada mu aiko da neman ginin Masallacin Juma’a sai munbi wadan nan ka’idoji, domin kuwa dama mun sani a Doka da kuma wannan sabon shirin gyaran kana nan Hukumomi, harkar Addini tana hannun Mai-girma Sarkin ne, wato Emirate Council wanda kumashine Shugabanta Allah ya taimakeshi ya kiyayeshi, amin. To dana gama yiwa wadan nan mutane bayani sai na tabbatar musu cewa nisansu da Masallacin Juma’ar garin Digacin kudai, bai kai yadda Shari’a da ka’idar gina Masallacin Juma’a ta ajiye ba, saboda haka ni bazan iya basu izinnin tara kudi don gina masallaci Juma’a ba, amma sa iya gyara masallacin don yim Salloli biyar kawai, amma ba Juma’a ba, domin kuwa ga masallacin Juma’a nan a kudi wanda nisansa dasu baifi kilometer 4-6 ba wadda yake dai dai da 2 ½ miles tsakaninsu. Kuma wannan Unguwa tana da yawan mutane, masu biyan haraji mutum 168. don haka idan suna shakkar wannan jawabi dana shaida masu sai su dawo gareni, na rubuta masu takarda ga mai-girma Sarkin Kano, don suji yadda wannan al`amari yake, kuma daga nan sai abinda Sarki yayi, domin kuwa ikon sa ne. Daga wannan lokaci ba wanda ya dawo gareni yayi mani wata magana daga cikinsu. .Ana cikin wannan hali ina sauraron mutanen nan, sai Mallam Ibrahim Karaye wanda yake shine jami`in aikin taimakon kai da kai na Karamar Hukumar Dutse a wannan lokacin yazo gareni(Hakimin Dutse), da cewa chairman na Dutse Local Government ya umurce shi yaje sabon garin Danmasara ya tambayesu ko suna son Masallolin Juma’a . Amma shi Mallam Ibrahim Karaye kafin yazo gareni sai da ya fadawa chairman gaskiyar yadda al’amarin ginin Masalincin Juma’a yake wanda ya tabbatar masa cewa ikon mai-girma Sarkin Kano ne tareda Majalisarsa. Saboda haka sai nace da Mallam Ibrahim Karaye tunda yake ya baka umurni, kai kuma kaga mutunci na saboda zamana Hakimin kasar kuma Wakilni mai-girma Sarkin Kano, kazo ka shaida mani sai kaje kayi abinda ya umarceka amma kuma ba tareda wani wakili na ba. Acikin wannan hali aka zauna ana cuku-cuku, har aka tara kudi daga Jama’a da sunan aikin taimakon kai da kai harma Dutse local Govt. Area ta bada irin nata taimakon duka dai akan Massalincin Jumma’a. Amma kuma Allah ya dade da ran Sarki ina tunawa a wata rana shi Chairman Alhaji Bashiru ya taba yi mani maganar za’a gina Massalincin Jumma’a a sabon garin Danmasara, harma na bashi amsa cewa mu Hakimai muna da umarnin mai-girma Sarkin Kano akan ka’idojin gina Massaslincin Juma’a wanda sai mun bisu sa’anan mun aika wa da mai-girma Sarkin Kano. To anan maganarmu ta tsaya baice kamai ba. Kuma Allah ya taimaki Sarki lokacin da mai girma Sarkin Kano yazo Dutse ran 15/12/1977AD. domin fasa Harajin 1977-78AD. Sarkin Shanu ya fada mani cewa Chairman na Dutse Local Govt. ya tabeshi da maganar ginin wannan Masalacin Juma’a na sabon garin Danmasara, amma abinda Sarkin Shanu ya baiwa Chairman amsa shine lallai subi ka’idar da Mai-girma Sarkin Kano ya aika wa da Hakimai. Don haka sai su shaidawa Hakimin Dutse. To tun daga wannan rana sukayi haka da Sarkin Shanu, Dutse Local Govt. bata taba yi mani wata magana ba akan wannan al’amari har zuwa yau 24/4/1978. Sai a ranar Juma’a 21/4/1978, na sami labari cewa Chairman na karamar Hukumar Dutse Alhaji Bashiru tareda yan-majalisarsa mutum biyu sune: - Alhaji Ibrahim Nakarofi, da Mallam Buba A. Sule Katanga, sunje sun bude wannan Masallacin Juma’a kuma sun nada Liman Mallam Isa Usman da Na’ibi Mallam Ali Musa, har ma Chairman ya basu Alkyabbu da Rawuna da Hulunan Dara dai dai ga Liman da Na’ibi, ba tareda sun sanar dani komai ba, game da wannan al’amarin, don haka ina cikin shakkar wannan Labari. Sai aran 23/4/1978AD. na bude Television ta Kano a labaran karfe 7pm. na dare na gidan Rediyo Telbijin Kano sai naji gidan Rediyon yana cewa:- Chairman na Karamar Hukumar Dutse, ya bude Masalacin Juma’a a Unguwar sabon garin Danmasara ta kasar Digacin kargo, ta kasar Dutse a ranar dana ambata a sama harma yayiwa Jama’ar wannan kasa ta Dutse gargadi da cewa su guji yada jita-jita gameda sha’anin Addini. Wadda nan take na tabbatar da gaskiyar labarin da na samu na bude wannan Masalacin Juma’a. Kuma ina kara tabbatarwa da mai-girma Sarkin Kano cewa dukkan wannan al’amari babu wanda ya sanar dani komai akai, don haka nake ganin an kaucewa ka’ida. Domin wannan ikon Sarkin ne. Don haka a ranar 24/4/2978, na tura aka kirawo mini Digacin kargo na yanzu Mallam Adamu da Mai-Unguwar Sabon Garin Danmasara, da malamin Digacin Kargo Alhaji Abdu Kargo dake zaune a wannan UNGUWA, da Limamin Masalacin Mallam Isa Usman, da Na’ibin Masalacin Mallam Ali musa. Don jin yadda wannan al’amari ya faru. A wannan rana ta 24/4/1978AD. Digacin kargo na yanzu Mallam Adamu yazo gabana tareda Alhaji Abdu kargo, malaminsa, da Mallam Isa Usman limamin Masalacin da Mallam Ali musa Na’ibin Masalacin. Da farko na tambayi Digacin kargo, da mutanen nan da suka zo da Digaci, cewa yaya akayi aka gina wannan Masalacin?. Kuma yaya akayi akanada Liman da Na’ibi, da kuma neman yadda akayi izinin fara yin sallar Juma’a acikin wannan Masalacin. Daga nan sai Digacin kargo tareda wadannan mutane suka shaida mini, (Hakimin Dutse), cewa sun tabbatar Chairman na Dutse Local Govt. Alhaji Bashiru tareda Yan-majalisarsa mutum biyu:- Alhaji Ibrahi8m Nakarofi, da Mallam Buba A. Sule Katanga sune suka bude wannan Masallacin, kuma shi Chairman ne ya nada Liman da na’ibi tareda basu dukkan kayan da ake baiwa Liman idan an nada shi. Kuma Digacin Kargo ya kara shaida mini (Hakimin Dutse), cewa Chairman na karamar Hukumar Dutse, Ya aika masa da sakon nemansa a wannan Unguwar ta sabon garin Danmasara don bude wannan Masalaci, amma shi Digaci da yaga babu hannun Hakiminsa na Dutse acikin wannan al’amari sai yaki zuwa, wannan gayyata ta Chairman. Saboda haka ba’a bude wannan Masalacin da shi Digacin ba. To daga nan sai na tambayi Liman Mallam Isa Usman cewa, yaya akayi lokacin da kuka zo gareni, da bukatarku ta ginin wannan Masalacin Juma’a inda na baiyana maku umarnin mai-girma Sarkin Kano, gameda ginin Masalacin Juma’a na kuma nemi shawararku cewa kwa iya gina Masalaci amma bana Juma’a ba saboda tsakaninku da kudai baikai yadda ake bukata a ka’idar ginin Masalacin Juma’a ba. Kuma na umurceku da cewa ku dawo gareni idan kun sanar da sauran mutanenku wannan jawabi dana baiyana maku don aikawa daku zuwa wurin mai-girma Sarkin Kano, daga nan ban sake ganinku ba, sai yanzu. Yaya akayi baku zo ba?. Sai Liman Mallam Isa Usman ya shaida mani cewa ai bayan mun koma gida sai Chairman na Karamar Hukumar Dutse ya aiki Mallam Ibrahim karaye, Shugaban Mai’aikatar aikin Taimakon kai da kai na Dutse local Govt. Area. Garemu ya shaida mana cewa Chairman Alhaji Basiru ne ya aiko shi garemu da cewar shi Chairman zai gina mana masallacin Juma’ar. Dajin haka sai na tambayi Liman mal. Isah Usman cewa ko lokacin da Chairman ya aiko Mallam Ibrahim Karaye gareku ya biyo takan Digacinku na Kargo, kokuma Mai Unguwarku? Sai Liman Mallam Isa Usman ya amsa mani cewa a’a shi Mallam Ibrahim bai biyo takan Digaci ko MaiUnguwaba, kai tsaye yazo gurinmu, ya shaida mana wannan umarni na Chairman. To sai na juya ga digacin Kargo cewa ko yasan lokacin da Mallam Ibrahim Karaye yaje gurin wadannan Mutane? Sai Dagacin Kargo ya amsa mini cewa ai shi bai san lokacinba kuma babu wanda ya sanar dashi, wannan magana sai lokacin da za’a bude Masallacin aka gayyaceshi, shi kuma yaki zuwa saboda babu yawun Hakimin Dutse a cikin wannan magana. To anan take nima kaina (Hakimin Dutse), na sake karantawa Digacin Kargo da wadannan Mutane takardar nan da Mai Girma Sarkin Kano daya aikawa Hakimai game da kaidojin gina Masallacin Juma’a. saboda haka na aiko da Digacin kargo, malamin Digacin Kargo Alhaji Abdu Kargo, da MaiUnguwar Sabon garin Dan Masara Mallam Wada Maigari, da Liman Mallam Isa Usman da Naibi Mallam Ali Musa ga Mai-girma Sarkin Kano, kuma sai abinda Sarki yayi akai, Allah ta taimaki Sarki ya kiyayeshi, Amin. Kuma na aika da kofen wannan takarda zuwa wajen Sakataren Karamar Hukumar Dutse, na kuma aikawa shi Sakataren karamar Hukumar Dutsen “True Copy” na takardun Mai-girma Sarkin Kano da muka sami umarnin Sarki, akansu game da kaidojin gina Masallacin Juma’a inda Maigirma Sarkin Kano, ya gargademu da cewa mu kula mu bi kaidar kamar yadda ya umarcemu dayi. Haka kuma ga “True Copy” nan nasu na aiko dasu ga Mai Girma Sarkin Kano wadda akansu ne Mai Girma Sarkin Kano ya aiko mana. Ata biyu mai lamba PUB/II/V/385 ta ran 26th Octoba, 1976AD. Kuma akan takardar aka shaida mana cewa an baiwa, Sakataren Karamar Hukumarmu kopen wannan takarda don sanarwa.
………………………………… District Head Dutse
No. 45/256A Dutse District Office Kano. 24/4/1978 The Secretary to, Dutse Local Government. Na aiko maka da kofen wannan takarda kofe biyu, tare da “True Copy” na umarnin Maigirma Sarkin Kano game da kaidojin gina Masallacin Juma’a da Sarki ya aikawa dukkan Hakimai, kuma atakardar Maigirma Sarkin Kano tagaremu mai lamba PUB/II/V/385 ta ran 26th Octoba 1976, ya baiyana mana cewa yaba Sakataren Karamar Hukuma kofen wannan takarda don sanarwa. Don haka na aiko maka da wannan bayani don sanarwa.
………………………………… District Head Dutse
Su kuma daga Kano sai suka ja hankalin Sarkin Dutse da karamar Hukumar cewa aiyuka irin wadannan daga ofishin Sarauta yakamata ayisu. Don haka sai suka kara tunasar dasu da wasikarsu mai lamba PUB/11/331 ta ranar 21st octoba 1975 daga ofishin madakin Kano da kuma mai Lamba PUB/11/V/385 ta ranar 26 octoba 1976 daga sakatariyar Majalissar Sarkin Kano.
Hakimin Dutse. MASALLACIN JUMA’ASanarwa gareka, ga al’ada kukan aiko da mutane gaban Sarki masu son suyi Masallacin Juma’a a Garinsu. Saboda haka daga yanzu anaso duk mutanen da suka nemi zasuyi Masallacin Juma’a ana bukatar kafin su aiko su tabbatar da: - 1. Nisan garin da za’ayi wannan Masallaci tsakaninsa da wani garin da yake da masallacin Juma’a. 2. Ka tabbatar da yawan Mutanen dake cikin wannan gari. To in ka tabbatar da wadannan san nan sai ka aiko dasu gaban Sarki tareda wannan bayani.
Snd (ALHAJI ALI HASHIM) FOR:MADAKIN KANO
True Copy: No. PUB/II/V/331 Kano Emirate Council Secretariat Kano. 26th Octoba,1976. Hakimin Dutse.
GINA MASALLACIN JUMA’AIna tuna maka da circular ta NO. PUB/II/VOL.V/331 ta ran 21/10/75 wadda nayi maka bayanin yadda ya kamata ka turo Mutane masu neman izinin gina Masallacin Juma’a kamar haka: - 1. Ka tabbatar da yawan Mutanen dake cikin wannan gari. 2. Ka tabbatar da nisan garin da za’ayi wannan Masallaci tsakaninsa da wani garin da yake da masallacin Juma’a akwai tazara. 2.To in ka tabbatar da wadannan sai ka aiko mutanen tareda wannan bayani. 3.Na aikawa da Sakataren Mulki na Karamar Hukumarku kofen wannan takarda don sanarwa.
Snd (ALHAJI ALI HASHIM) FOR:MADAKIN KANO
Ana nan sai Siyasar 1979 ta shigo kuma a Jihar Kano da Dutse take karkashinta a zaben da’akayi na 1979 P.R.P. ce taci zabe. Aka zabi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya zama zababben Gwamnanta na farko P.R.P. dayake gyauron N.E.P.U. ce tsarinta na Kawo Canjine. Musamman akan Sarakuna. Wannan yasa ranar da aka rantsar da sabon Gwamnan na Kano Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya fara da soke haraji da jangali, kuma ta sauke zababbun shugabannin kananan Hukumomi ta nada wakilan riko don su aiwatar mata da manufofinta. A Dutse Alhaji Adamu Barde Dutse shi ya shugabanci kwamitin rikon. Shi kuwa dama tsakaninsu da wanda ya gada Shugaban Karamar Hukumar nada Alhaji Basiru Kamar tsakin da tsakuwa saboda Alhaji Basiru Dutse N.P.N. ya goyi baya a lokacin zaben da aka yi na 1979. Zababben Gwamnan Kano na farko Alhaji Abubakar Rimi ranar Juma’a 1 ga watan Aprilu 1981, yayiwa Jama’ar Kano jawabi cewa “A tsare-tsarenta na kawo canji, Jam’iyar P.R.P. ta nada sabbin Sarakuna masu Martaba ta daya guda hudu (4) kuma ta daga Martabar garuruwansu zuwa Martabar Masarautu. Garuruwan sune: - Dutse, Gaya, Auyo da Rano. Kuma ta daga Martabar Masarautun Kazaure da Gumel masu Martaba ta biyu zuwa Martaba ta daya tare da Garuruwansu. Daga baya kuma aka daga Martabar Masarautar Hadejia da Sarkinta zuwa masu daraja ta daya. A takarda mai lamba COS/A/181/T.1/3 ta ranar 6 ga watan Aprilu 1981, wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Sule Yahaya Hamma ya sawa hannu ta sanarwa da Hakimin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano Dutse cewa Gwamnatin Kano ta daga matsayin wasu Hakimai zuwa Masarautu masu daraja ta daya. Wadda Dutse take ciki.
Alhaji Abdullahi Maikano Dutse, Emir of Dutse. Mai girma, DAGA MARTABA DA NADAKA SARKI MAI DARAJA TA DAYA “EMIR” Daga irin alkawaran Gwamnatin Kano na kyautata rayuwar jama’arta da basu hakkinsu da Martabarsu, Gwamnatin Kano karkashin shugabancin Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, batabar bangaren Sarautaba domin ta duba Tarihin da asalin wasu garuruwa da suke da yancinsu tun asali amma saboda tsari irin na yan mulkin mallaka suka maidasu karkashin wasu Sarakuna wai dan suji saukin mulkinsu. Ganin haka Gwamnan Kano Alhaji Muhammad Abubakar Rimi da Gwamnatinsa bayan dogon bincike akaga ya dace a dawowa da garuruwan GAYA, DUTSE, AUYO DA RANO Martabarsu.Don haka ina sanar maka Gwamnan Kano Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya daga Martabar kasarka kuma ya nada ka Sarki mai daraja ta daya. Karkashin bangare na 5 na dokar nadin Sarakuna. Kuma daga baya za’a sanar maka da ranar da Maigirma Gwamnan Kano zaizo ayi bukin baka sandar Girma a Dutse. A madadin maigirma Gwamnan Kano da Jama’ar Jihar kano ina tayaka murna da farincikin samun wannan sabon mukami. Allah ya baka ikon kyakkyawan Jagoranci.
Alhaji Sule Yahaya HammaSakataren Gwamnatin Jihar Kano. Don haka Gwamnan Kano yayi bukin nadasu kamar haka: - 1. Ranar Juma’a 29 ga watan Mayu 1981, aka nada Alhaji Ahmad Muhammadu Sani Sarkin Gumel mai daraja ta daya. 2. Ranar Asabar 30 ga watan Mayu 1981, aka nada Alhaji Aliyu Sambo Hakimin Auyo ya zama Sarkin Auyo mai daraja ta daya. 3. Ranar Juma’a 5 ga watan Yuli 1981, aka nada Alhaji Abdullahi Maikano Dutse Hakimin Dutse ya zama Sarkin Dutse mai daraja ta daya. 4. Ranar Juma’a 12 ga watan Yuli 1981, aka nada Sanata Alhaji Adamu Gaya a matsayin Sarkin Gaya mai daraja ta daya. 5. Ranar juma’a 19 ga watan Yuli 1981, aka nada Alhaji Abubakar Ila Hakimin Rano ya zama Sarkin Rano mai daraja ta daya. 6. Ranar Asabar 5 ga watan Satumba 1981, aka nada Alhaji Ibrahim Adamu Sarki mai daraja ta biyu zuwa mai daraja ta daya. 7. Daga karshe aka nada Alhaji Maje Haruna Sarkin Hadejia mai daraja ta biyu zuwa mai daraja ta daya. Zamewar Hadejia ita ta zamo ta karshe bai rasa alaka da zamewar su cikakkun masu goyon bayan N.P.N. neba. Ita kuwa Gwamnatin P.R.P. bata yafiya akan banbancin ra’ayi koda cikin yan jam’iyarne. Ammadai hakuri yayi ranarsa domin Hausawa sunce Mahakurci Mawadaci. Domin da akayi Jihar Jigawa Hadejia ita ta zama mazaunar Shugaban Majalissar Sarakunan Jihar Jigawa. Daga ranar 5 ga watan Yuli da mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Abdullahi Maikano ya karbi sandar girma da wukar yanka a hannun zababben Gwamnan Kano na farko Alhaji Abubakar Rimi sai abubuwa suka fara canzawa. Sarki ya nemi yan uwa da abokan arzuka su hadu su taimaka masa wajen tafida wannan sabon aiki ga Jama’arsa. Wannan yasa Sarkin yayi nade-naden Sarautu ga yan uwa. Hakika wannan abu da yayi ya kara zumunci. ZABEN SIYASA NA 1983AD. Lokacin da akayi zaben Siyasa na 1983AD. Alhaji Sabo Aliyu Bakin Zuwo ne yaci zaben Gwamna. A tutar Jam’iyyar P.R.P Nasara kuma kamar yadda akaga a baya ya zama mai biyayya ga Masarautar Kano. Duk abinda zaiyi yakan tuntubi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero kuma itama MaSarautar kano tazama tana tare da Gwamna. Wannan yasa sabon gwamna bayan ganin Gwamnatinsa ta zauna sai ya fara da rushe sabbin masarautun da tsohon Gwamna Alhaji Abubakar Rimi ya kirkiro na Gaya, Dutse, Rano da Auyo ya kuma bada umarnin su koma matsayinsu na Hakimai karkashin masarautunsu nada Haka akayi, kuma su da aka tube suka yarda su zauna hakan. Sun rungumi kaddara. Wannan abu yayi wa Sarkin Kano da MaSarautarsa dadi. Kuma yasa suka kara sa ido akan wadannan rusassun Sarakuna. Kuma da yake lokacin Siyasa ne, ita kuma Siyasa tana da adalci. Daga cikin adalcin Siyasa ya hada da duk inda ta dagaka sai ta saukeka, kamai dadin da tabaka sai kaji dacinsa, saita nuna maka indai don Duniya ka daura damara to ka kwance, duk irin gabar da Mutum ya dauka wani lokaci zaizo a ware, watakila ma sai yasa wasu suke cewa “A Siyasa ba’a tabbataccen Gaba” domin wata rana za’a iya dawowa a zauna inuwa daya kamar ciki daya. Kuma dama Sarkin Dutse Abdullahi Mai-Kano yayi Siyasa don haka sai yabi tsarin Siyasa a hankali. Yabi gwamnati yabar wasu ‘yan uwan sa. A wannan tsari kuma wasu daga cikin ‘yan uwan nasa irin su Alhaji Aminu Sulaiman dan uwansa na Jini basuji dadin shrin na Sarki Abdullahi Maikano ba. Daga karshe ranar 20 ga watan Agusta 1983AD. Gwamnatin Kano ta hannun Masarautar Kano tayi wa Alhaji Abdullahi Maikano Sarkin Dutse ritaya. Sarkin Dutse Alhaji Maikano yayi shekara Ashirin da uku (23) yana Sarautar Dutse 1960- 1983. ya koma Hotoro ta Kano da zama kuma acan Allah yayi masa rasuwa a ranar Laraba 27 ga watan yuli 1987, shiyasa ake ce dashi Maje Hotoro. Allah yajikansa ya gafarta masa. Amin. 2.17 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA BAKWAI (17) ALHAJI MUHAMMADU SANUSI DAN BELLO 1983-1995AD. (BAJALLIBE) Sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Sanusi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ne ya nadashi Sarkin Dutse ranar Litinin 31 ga awatan Octoba 1983 AD. Kafin ya zama Sarki, Alhaji Muhammadu Sanusi yayi Sarauta hawa-hawa a wuri daban-daban. Yayi digacin Gurum Galamawa 1937-1943AD, digacin Yargaba 1943-1953AD, Digacin Gurduba 1953-1981AD. a wannan 0lokaci duk inda aka kaishi ana kaishine domin gyara saboda wasu guraren Barayi sun damesu, wasu guraren kuma fitinune suka damesu. Kuma cikin ikon Allah sai aga an samu biyan bukatar da aka kaishi domin ta, gurare sun zauna lafiya. Sarautar wannan Sarkin Dutse wata iri ce da zata karawa mai Imani Imani tasa mai raunin Imani ya jaddada kuma ya karfafa Imaninsa, kuma wanda bashi da Imani ya zama mai Imani. A lokacin Alhaji Adamu Barde Shugaban riko na Karamar Hukumar Dutse na farko da Gwamnan Kano na farko ya nada tare da amincewar mai Martaba Sarkin Dutse an yiwa Digacin gurduba Alhaji Muhammadu Sanusi Ritaya daga Digaci. A ganin wasu Mutane anyi wannan don musgunawa Alhaji Basiru Dutse zababben shugaban Karamar Hukumar Dutse na farko, Wasu kuma suna gani a`a anyi ne domin a kakkabe hannun Alhaji Muhammadu Sanusi da zuriyarsa daga tsarin Sarautar Dutse gaba daya. Domin afahimtar wasu Alhaji Muhammadu Sanusi Mutum ne tsayayye kuma yasa Sarautar Dutse a ransa wadda suke ganin lallai yana so yayi. Da aka yi masa Ritaya sai aka tura wani yaron Gidan Sarki Garba Dangulili yayi wakilci da zummar a bata wa Alhaji Muhammadu Sanusi, amma sai Allah ya canza shirin, Garba Dangulili yabi tsarin a hankali da fuska biyu, don a zauna lafiya. Wannan kuma yayi wa wakilin kyau. Domin da aka samu canji kamar yanda za’a gani a gaba sai shi Garba Dangulili yazama anayi dashi. Harta kai ya zama shamaki a fadar sabon Sarkin Dutse daga karshe. Wannan ritaya da aka yiwa Dagacin na Gurduba ta bata rai da kyau. Domin har MaSarautar Kano da Sarkinta Alhaji Ado Bayero basuji dadi ba. Don haka saboda soyayya Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero duk sanda murabus Alhaji Muhammadu Sanusi yaje gaisuwa ko kuma shi Sarki Kano yayi tafiya ya tsaya a Shuwarin don su gaisa ya kan cewa murabus Allah ya kyauta hakuri. Shi kuma Murabus yace “Amin" Lokacin da akayi zaben Siyasa na 1983AD. Alhaji Sabo Aliyu Bakin Zuwo ne yaci zaben Gwamna. A tutar Jam’iyyar P.R.P Nasara kuma kamar yadda akaga a baya ya zama mai biyayya ga Masarautar Kano. Duk abinda zaiyi yakan tuntubi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero kuma itama MaSarautar kano tazama tana tare da Gwamna. Wannan yasa sabon gwamna bayan ganin Gwamnatinsa ta zauna sai ya fara da rushe sabbin masarautun da tsohon Gwamna Alhaji Abubakar Rimi ya kirkiro na Gaya, Dutse, Rano da Auyo ya kuma bada umarnin su koma matsayinsu na Hakimai karkashin masarautunsu nada Haka akayi, kuma su da aka tube suka yarda su zauna hakan. Sun rungumi kaddara. Wannan abu yayi wa Sarkin Kano da MaSarautarsa dadi. Kuma yasa suka kara sa ido akan wadannan rusassun Sarakuna. Wannan yasa mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya cika addu’arsa da yake yiwa Alhaji Muhammadu Sanusi ta Allah ya Kyauta hakuri. Ya nadashi Hakimin Dutse ranar 31 ga watan oktoba 1983AD. Sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Sanusi, da kama aikinsa na Hakimi sai ya cigaba da tsarin yadda za’a zauna Lafiya a kasarsa ta Dutse. Kuma ya cigaba da ganin ansa yara a Makaranta tare da ganin karamar Hukumar ta cigaba da taimakawa makarantu da kayan aiki. Daga nan sai yayi karatun baya yatausayawa Digatan da aka sauke lokacin Mulkin Sarkin Dutse Abdullahi Maikano ya dawo dasu kan mukamansu. Ya kuma cigaba da kyautata zumunci tsakaninsa da yan uwa, Da biyayyarsa ga Sarkin Kano Alhaji Ado bayero. Allah yayiwa mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Sanusi rasuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, anyi Jana’izarsa a cikin Garu aka kaishi gidansa na shuwarin aka binneshi acan. 2.18 SARKIN DUTSE NA GOMA SHA TAKWAS (18) ALHAJI NUHU MUHAMMADU SANUSI (BAJALLIBE) 1995 – DATE Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi ya zama Sarki “Emier” ranar 11 ga watan Disamba 1995. Wannan ya biyo amincewar da gabatar dashi da masu zaben Sarki na MaSarautar Dutse sukayi ga majalissar Sarakunan Jihar Jigawa bisa la’akari da dokar nada ko tube Sarakuna ta jihar Jigawa mai lamba 3(2) ta 8 ga watan Nuwamba, 1995 AD. Wadda kantoman mulkin soja Kanar Ibrahim Aliyu ya sawa hannu ran 28 ga watan Nuwanba, 1995. A). Majalissar Sarakunan Jihar Jigawa bayan tasa albarka ta mikawa Gwamnatin Jihar Jigawa karkashin shugabancin Kantoman Mulkin Soja Kanar Ibrahim Aliyu, wadda ya amince da nadin Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi Sarkin Dutse Sarki mai daraja ta daya Wannan nadi nasa yanuna yasha bam-bam da nadin sauran Sarakuna goma sha bakwai (17) da suka gabata saboda shine Sarki na farko da masu zaben Sarki suka zaba sauran duka nadasu akayi B). Masu zaben na Sarkin Dutse sun mikawa majalissar Sarakunan Jihar Jigawa sunayen wadannan mutane guda uku (3) da suka samu kuri’a dan dubawa da bawa Gwamnati shawara da amincewa da daya daga cikinsu domin a nadashi Sarki mutanen uku da aka mika sune: - Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi Ciroman Dutse, Alhaji Basiru Muhammadu Sanusi Galadiman Dutse da Alhaji Nuhu Abdullahi Maikano Danmajen Dutse. C). Kantoman Mulkin Soja Kanar Ibrahim Aliyu bisa la’akari da matakan da aka bi a sama A&B, kuma Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi ya zama shi yafi sauran yawan kuria. Kantoman ya amince da Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi ya zama Sarkin Dutse Kuma Gwamnatin Jihar Jigawa tayi bukin nadashi da bashi sanda tare da rantsar dashi amatsayin Sarkin Dutse ranar 11 ga watan Disamba 1995. FANNIN MULKI Ta bangaren Mulki saboda gogayyar daya samu ta rayuwa da zamansa a cikin mulki Sarkin Dutse Nuhu Muhammadu Sanusi ya sakewa MaSarautar Dutse fasali ya sake tsara masu zaben Sarki, ‘yan majalissar Sarki aka kara yawan Gundumomi da Hakimai, Digatai da masu Unguwanni don kusantar da Sarauta ga Jama’a don asamu cigaba. Sarki Alhaji Nuhu Sanusi yayi nade – naden Sarautu da Sarakunan fada tare da tsarin Matan Fada da Marokan Fada dan ya daidaita fadarsa da sauran Fadoji. Masarautar Dutse a halin yanzu tanada Hakimai masu kasa guda Ashirin (20).
YAWAN HAKIMAI, DIGATAI DA MASU UNGUWANNIN MASARAUTAR DUTSE
GUNDUMOMIN MASARAUTAR DUTSE Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi bisa tsakaninsa da biyayyarsa ga Gwamnati yayi shawara kuma a wani lokaci ya karbi umarni wajen duba Karin gundumomi da nadin Hakimansu daga gwamnatiSaboda cigaban Jama’arsa. Wannan yasa aka sami Karin Gundumomi da Hakimai masu kasa guda goma sha biyar (15) kari akan guda biyar (5) da ya tarar. Gundumomin suka zama guda Ashirin (20) da Hakimai guda Ashirin (20). GUNDUMOMIN DAYA TARAR SUNE: - 1. Dutse a karamar hukumar Dutse 2. Birnin Kudu a karamar Hukumar Birnin kudu 3. Jahun a karamar hukumar Jahun 4. Gwaram a karamar Hukumar Gwaram 5. Kiyawa a karamar Hukumar Kiyawa. SABBIN GUNDUMOMIN DA HAKIMAN DA AKA KARA SUNE: - 1. Chamo, Dundubus da Sakwaya a Karamar hukumar Dutse. 2. Sundumina, Iggi da Wurno a Karamar hukumar Birnin Kudu. 3. Fagam da Basirka a Karamar hukumar Gwaram. 4. Aujara da Gunka a Karamar hukumar Jahun. 5. Zareku a Karamar hukumar Miga. 6. Shuwarin a Karamar hukumar Kiyawa. 7. Buji a Karamar hukumar Buji, saboda anan dama garin Buji aka bawa sunan Karamar hukumar mai cibiyarta a Gantsa kuma buji ta zauna a mukamin digaci kafin nadin Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi. |
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|