|
|
|
Manufar Masarautar Dutse na bude wanna bangare shine burin biyan bukatar da manema tarihi suke da ita akan Dutse tun kafa Jihar Jigawa ta Nigeria mai cibiya a Dutsen. Dutse (Gadawur) boyayyen garine ga mutane da yawa in banda makaranta tun a tsohuwar Jihar Kano, don haka ya zamo abin mamaki sanda Shugaban kasar Nigeria Janar Ibrahim badamasi Babangida ya sanar da kirkirar Jihar Jigawa mai Babban birni a Dutse. Mutane da yawa sunyi suruce-suruce akan sa babban birnin Jihar Jigawa a Dutse saboda a wannan lokacin a kwai manyan garuruwa kamar su Hadejia, Gumel da Kazaure a cikin Jihar. Tarihi ya nuna Dutse (Gadawur) na cikin garuruwa masu tarihi da za'a iya kwatance dasu a tsohuwar Jihar kano, a hakikance Dutse ke biye bayan Birnin Kano. mazaunan Dutse sun zamo gwamutsen al'umma tun kafin karni na 15, a cikin al'ummar da suka hada garin Dutse sun hada da Fulde (Genawa), Wangarawa (kanuri), Hausa (Digawa). Birnin Gija wanda yake kilomita kadan a yamma da garin Dutse sananne ne ga masana tarihi wajen kasuwanci a wajen birnin Kano. Yakin saifawa na El-kanemi ya kwace mulkin Gazargamu wanda ya janwo gudun hijirar fulani da yawa zuwa Dutse wanda suka kunshi kabilar Jalligawa da Yalligawa. Garin Dutse yaci gaba da zama a gari marar yanci kafin Jihadin Usman dan Fodiyo, zuwan Fulani wanda suka fara mulkar Dutse ya soma daga darajar garin lokacin nadin Sulaimanu sarkin Sokoto. Inda garin Dutse yake shi ya karawa garin tsaro kuma ya bada ishasshen gun horon mayakan garin. Na gayyaceka ka duba wannan shafi (yanar gizo) don samun tarihin wannan Masarauta dazai gamsar dakai. Sannan kana da damar bada taka Gudummawar ko gyara akan wannan Tarihi. |
|
|