|
|
|
GUNDUMOMIN MASARAUTAR DUTSE GUDA ASHIRIN DA TAKAITATTUN TARIHINSU. MAJALISSUN KANANAN HUKUMOMIN MASARAUTAR DUTSE DA HAKIMANSU Gundumar Dutse tayau itace cibiyar MaSarautar Dutse ta yanzu. Don haka kamar yadda wannan dan littafi ya nuna tun farko Dutse nada dogon tarihi daya fara tun 1450, kuma shugabancin Dutse ya far 1727 inda wani Dattijo mai suna Tsohon-Mutum ya fara shugabancin Dutse daga baya wasu Fulani guda biyu Salihi da Musa da suka zo daga wajen Borno suka karbi mulkin Dutse. Gundumar Dutse ta yanzu itace mazaunin cibiyar Karamar Hukuma ta yanzu kuma Tarihin shugabancinta ya nuna Hakimai in za’a koma tun farko Hakimai Goma sha Takwas (18) suka mulki Dutse. Bayan kirkiro Jihar Jigawa a 1991, Dutse ta zama maSarauta, kuma mulkin gunduma ya canza Dutse ta canja zuwa karkashin mulkin Sarkin yanka. Tun daga samun wannan daga daraja ta Dutse wadannan mutane suka mulki Dutse a matsayin gunduma, karkashin Hakimi. 1. Alhaji Basiru Muhammadu Sanusi galadiman Dutse 1991 – 1993. 2. Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi Ciroman Dutse 1993 - 1995. 3. Alhaji Shehu Muhammadu Sanusi Ciroman Dutse 1995 - …… Gundumar Dutse nada Digatai Goma sha Bakwai (17) da masu unguwanni Dari da biyu (102). Digatan sune: - 1. Dutse cikin gari 2. Limawa 3. Kachi 4. Madobi 5. Kargo 6. Kwaimawa 7. Kudai 8. Baranda 9. Kasarau 10. Hammayayi 11. Fanisau 12. Galamawa 13. Larabawa 14. Malamawa 15. Kwadiya 16. Yalwa 17. Kwarin Makera Hakimin Dutse Alhaji Shehu Muhammadu Sanusi ya tasamma Bunkasa addinin Muslinci ta hanyar kokarin bawa talakawansa Ilmin. Ta harkokin ilmin zamani Hakimin na Dutse ya tasamma taimakawa samari don su samu kyawawan takardun fita daga sakandire don su shiga Ja’mia. Sukuma manya, Alhaji Shehu Muhammadu Sanusi ya tasamma basu ilmin yaki da Jahilci da ilmin sana’a. Wannan Karamar Hukuma ta kunshi Gundumomin Dutse, Chamo, Dundubus da Sakwaya kafin su zama kananan Hukumomi. Wadannan gurare suna alfahari da ‘ya’yansu da suka taimaka wajen daukaka ko bunkasa wadannan bangarori ta hanyoyi daban-daban, kodai ana lokacin gwamnatin Arewa tada ko Jihar Kano tada ko Jihar Jigawa ta yanzu. Wadannan taimako nasu ya faru lokacin da suka rike mukaman Gwamnati ta hanyar samawa ‘yan wannan bangare abin yi ko ta neman Jihar Jigawa tun asali, ko neman kananan Hukumominmu na yanzu kokuma neman Gundumomi don bun bunkasar garuruwanmu. Wadannan ‘ya’ya na wannan bangare sun hada da: - 1. Marigayi Alhaji Isah dan Aminu – Tsohon Sakataren Firimiyan Jihar Arewa na farko Alhaji Sir. Ahmadu Bello. 2. Alhaji Inuwa Dutse – Tsohon kwamishinan Jihar Aikin Gona na Jihar Kano, kuma Jagoran neman Jihar Arewa. 3. Marigayi Alhaji Isah Gambo Dutse – Tsohon Sakataren Jihar Kano, kuma shugaban Ma’aikatar daukan Ma’aikata ta Jihar kano. 4. Alhaji Abba Dutse – Tsohon Sakataren Ministan Aikin Gona na Jihar Arewa, Tsohon Sakataren Gwamnan Jihar Kano Alhaji Audu Bako, Tsohon Sakataren MaSarautar Dutse, kuma Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar daukar Ma’aikata ta Jihar Jigawa. 5. Marigayi Alhaji Muhammadu Isma – Tsohon Shugaban Ma’aikatar sayen kayan Gona na Jihar Kano. 6. Alhaji Muhammadu Adamu – Tsohon kwamishinan lafiya na Jihar Kano kuma Tsohon Shugaban Ma’aikatar raya Birnin Dutse Jihar Jigawa. 7. Alhaji Sale Ciroma Sakwaya – Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sufuri ta Jihar Jigawa. Kuma Hakimin Gundumar Chamo. 8. Alhaji Basiru Dutse – Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Dutse na farko. 9. Alhaji A.V.M. Muktari Muhammad – tsohon Gwamnan Mulkin Soja na Jihar Kaduna, Ministan Ayyuka na tarayyar Nigeria, kuma Shugaban kwamatin kwato da binciken dukiyar Jama’a a lokacin Gwamnatin Murtala. 10. Alhaji Farouk Ahmad – Tsohon Shugban Bankin Tropical Bank, Kwamishinan Ciniki na Jihar Jigawa, kuma Madakin Dutse. 11. Alhaji Bashir Dalhatu – Tsohon Minista mai tarihi da yayi Minista sau hudu (4) a gwamnatocin mulkin Soja kuma Shugaban Bankin raya Aikin Gona na Nigeria. 12. Alhaji Ilyasu Sa’idu Dundubus – Tsohon Shugaban Majalissar Jihar Jigawa. Garin Chamo garine na Bare-Bari mai tsohon tarihi wanda wasu mutanen Machina suka kafa. Sarkin Chamo na farko wani Babarbarene mai suna Muhammadu Girema. Wadannan Mutane su suka shugabanci Chamo: - 1. Muhammad Girema 2. Dan Darman Maje Gantsa wanda Sarki yatashe shi daga Chamo saboda yawan Hari da ake kaimasa ya koma kan iyakar Dutse da Birnin kudu.. 3. Sarkin chamo Ibrahim sarikwai dandarman Maje Gantsa shi ya gaji dandarman maje Gantsa. 4. Sarki Isa kanin Sarkin Gunka 5. Sarki Musa dan Sarkin Chamo Gerema. 6. Sarkin Chamo Muhammadu Dan Ya’u. Ranar 29 ga watan Fabrairu 2000 Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu sanusi ya daga Martabar garin Chamo daga Digaci zuwa Hakimi. Hakiman Chamo Sune: - 1. Alhaji Musa Abubakar Gwaram magajin Mallam 29/2/2000 – 27/2/2001. 2. Mallam Tijjani Abubakar dan Musa 28/2/2001 – 8/9/2002. 3. Alhaji Sale Ciroma Sarkin Fadar Dutse 8/9/2002 - … a lokacinsa aka samu Karamar Hukumar Chamo. Gundumar Chamo tana da Digatai Takwas (08) Digatan takwas Sune: - 1. Chamo 2. Chai-chai 3. Abaya 4. Dagwaje 5. Kyaran 6. Isari 7. Tabobo 8. Wurma
Garin Dundubus garin fulanine kuma ya samu sunansa daga kalmar Kusaci “Dundubus” ma’anar su nan nan ko kusannan. Hakan tafaru saboda da garin unguwace karkashin digacin duru. Ance duk wanda zaije sai yace yatafi unguwar Dundubus. Daga baya akayi ayaga aka bawa mai garin Dundubus Digaci. Dama da digacin duru Sarki Usman da digacin Dundubus saboda akayi Sarki Sulaimanu wane da kani. Sarki Sulaimanu Bafulatanine kuma maharbi wanda yayi suna akan kokarin tsaro, ance kullum da daddare sai yazagaye kasarsa shi kadai wannan tasa alokacinsa ba’a Sata, ba’a tashin Hankali kuma fitunu sun ragu kwarai da gaske a Dundubus. A lokacin mulkinsa an samu cigaba wajen bawa kasar Ilimin yaki da Jahilci dana Firamare. Yayi shekara Hamsin da Takwas (58) kafin Allah yayi masa rasuwa a shekara ta 1981. Bayan rasuwar Sarki Sulaimanu sai Sarki Babawuro Sulaimanu wanda yayi shekara uku (3) yana Digacin Dundubus shima ya rasu. Daganan sai Sarki Adamu Usaini wanda aka nadashi a cikin shekara ta 1984. yana da shekara Goma sha tara (19) yana dagacin garin Dundubus ya samu cigaba zuwa mukamin gunduma a cikin shekara ta 2002, aka nada Alhaji Saidu Zakariyya Hakimin dundubus na farko. Gundumar Dundubus nada digatai kamar haka: - 1. Dundubus 2. Kacha 3. Zangon buji 4. Yalwa 5. Buju 6. Warwade 7. Jidawa 8. Dutsin Buju 9. Karnaya 10. Yargaba 11. Darau 12. Wangara
Sakwaya wani garine yamma da cibiyar MaSarautar Dutse. Wannan babban gari mai tarihi ya samu sunansa daga wata Aljan mai suna “SAKWAYA”. Anayiwa garin sakwaya lakabi da sakwaya-jamban domin a banbantata da Sakwayan Takwai da ake kira Sakwayan yan-Sarki. Wannan Aljana sakwaya ta zauna a “Sadai da Tani” wasu unguwoyine karkashin sakwaya da garin digacin Gadarowa kafin ta zauna a wurin da aka kafa sakwaya ta yanzu. Garin Sakwaya nada ganuwa da take da kofofi da ake kira kofar Gabas, Kofar Yamma, Kofar Kudu da Kofar Arewa. Kuma duk kansu suna da kyamare. Garin na Sakwaya ya Shahara wajen kasuwanci domin yana da babbar kasuwa a “Rigoji” wadda har daga Faranshi da asham ake zuwa sayayya cikinta kuma Jama’ar sakwaya sun shahara wajen yakin Kibiya, Mashi, Barandami da gariyo. Kuma ba’a taba cin sakwaya da yakiba. Garin Sakwaya yana da wasu bishiyoyi da mutanen garin da suka yarda dasu wajen idan sunyi kuwwa halamune na faruwar wasu abubuwa. Misali alamar zuwan abokan gaba. Bishiyoyin kukokine da ake kiransu da TASKIRA, da take a yamma maso gabas da garin Jilo da ake kiranta da sunan wani tsohon Mutum mai shekara dari da hamsin (150) itama tananan dungun garin gabas maso kudu. Mutanen sakwaya ance da anyi maganar su sai suji kamar an tadasu a tsimi. MUTANEN SAKWAYA Mazauna sakwya na farko kafin zuwan Shehu Usman Danfodiyo Hausawane, amma da zuwan Usman dan Fodiyo ya turo wasu Fulani Malamai ADANSU DA JABBO don su koyawa Mutanen Sakwaya Addinin Muslinci. Wasu daga cikin Maguzawan suka bar garin wasu kuma suka karbi addinin Muslinci. Suka nada Malam Adansu ya zama Limaminsu. Har yanzu wadannan Zuria ke limancin Garin Sakwaya. MULKIN GARIN SAKWAYA Kamar yadda muka ga abaya cewa zuwan su Adansu da Jabbo Hausawa su suka Shugabanci Sakwaya. Daga baya Mallam Jabbo da zuriyarsa (watau Fulani) suka karbi shugabancin garin na Sakwaya. Mutane irinsu Mallam Jabbo, Mallam Yahaya, Mallam Ibrahim I, Makama Alu, Mallam Amadu, Mallam Ibrahim II, mallam Safiyanu da Mallam Shehu daga zuriar Jabbo sun shugabanci garin Sakwaya harma daga karshe an sami mallam sale Ciroma daga cikin wannan zuri’a ta Fulani da aka nada Hakimin, amma shi an kaishi Gundumar Chamo. Hakimin sakwaya na farko shine Alhaji Muhammadu dan Kwano Jahun, wanda Sarkin Dutse yanadashi a ranar….… . Wannan Mutum Dattijone irin mutanen jiya da basa gajjiya, kuma koda yaushe cikin aiki yasa agabansa. A lokacinsa sakwaya ta samu Karamar Hukuma. Gundumar Sakwaya karkashin mulkin wannan dattijo nada Digatai Takwas (8) masu Unguwanni arbain da uku (43) digatan guda takwas sune: - 1. Sakwaya Gari 2. Tesa 3. Gadarawa 4. Dan tawuya 5. Ruru 6. Jaudi 7. Zobiya 8. Jigawar tsada.
Birnin kudu tsohon garine mai tsohon tarihi, amma dalilin da yasa ake kiran garinda birnin kudu shine. Wata macece babar bariya yar Sarkin Borno mai suna Maryam kan hanyarta ta tafiya Zazzau sai ta hadu da ciwon maruru da ake kira “Kudu” yakada ita ta jima bata warkeba. Lokacin wannan lalura ta “Kudu” Maryam ta zauna a wata Kamfa (Dutsi) a zarenawa kusa da kofar shiga garin Birnin kudu ta gabas da ake kira Bodan. Data samu sauki zata tafi sai tace wannan gari shine Birnin kudu wato Birnin maruru a Barbarce. Daga karshe aka gyara fadar sunan da hausa akece da garin Birnin kudu. B/kudu tana daya daga cikin gundumomi ashirin da suka hadu suka zama MaSarautar Dutse. Tana kudu da Dutse misalin Mil talatin (30) ko kilomita Hamsin (50) kan hanyar Borno da Bauchi. Al ummar Birnin kudu sunfi magana da harshen Hausa duk da suna cakude da Fulani da bare-bari. Kuma Sana’oinsu sun hada da Farauta, Kiwo, Noma da kasuwanci. SARAKUNAN GUNDUMAR BIRNIN KUDU Sarakunan gundumar Birnin Kudu suna da yawa amma wadanda aka san tarihinsu da yawan shekarun da sukayi suna Sarauta guda shidane wato: - 1. Sarkin Kudu Muhammadu 1894 – 1927, shekara talatin da uku (33). 2. Sarkin Kudu Saleh 1927 – 1932, shekara 25 3. Sarkin Kudu Yakubu 1952 – 1975, shekara 23 4. Sarkin Kudu Datti 1975 – 1984 shekara 9 5. Sarkin Kudu Lamido 1985 – 1999 shekara 14 6. Sarkin Kudu Hassan Jibrin 1999 – ….. Birnin Kudu nada Digatai Ashirin da Hudu kamar haka: - 1. Zarenawa 2. Masaya 3. Unguwar Fada 4. Lafiya 5. Jigawar Nasara 6. Badungu 7. Kiyako 8. Mada kudu 9. sarko 10. Kangire 11. Damu 12. Kura 13. Bigidan 14. Kafin Gana 15. Zanga 16. kantoga 17. Chagu 18. Masamawa 19. Zaraina 20. Zazika 21. Juwa 22. Shawu 23. Waza 24. Jigawar Tokare Karamar Hukumar Birnin kudu data kunshi Gundumomin Birnin Kudu, Iggi, Sundimina da Wurno na farin ciki da wadannan ‘ya’ya nasu: - 1. Alhaji Da’u Aliyu – Tsohon Malamin Makaranta, Kwamishinan kananan Hukumomin Jihar kano. 2. Alhaji Dr. A.T. Ayuba – Tsohon malamin Makaranta a matakai daban – daban har zuwa Jami’a kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa a zamanin mulkin Sojoji. 3. Alhaji Sule Lamido – Tsohon dan Majalissar tarayyar Nigeria, Ministan Harkokin Kasashen wajen Tarayyar Nigeria, kuma dan takarar gwamnan Jihar Jigawa. 4. Alhaji Ali Sa’adu – Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa. 5. Alhaji Sabo Wurno – Tsohon malamin Makaranta, kuma Hafsan Sojojin Jiragen Sama. 6. Alhaji Garba Yalwan Damai – Tsohon Malamin Makaranta, Sakataren Ma’aikatar tura Dalibai karo Karatu, Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birini Kudu, Kuma dan Majalissar Jihar Jigawa 7. Alhaji Sabo Sundumina – Dan Kasuwa, kuma dan Takarar Gwamnan Jihar Jigawa a tutar Jam’iyyar ceton Talakawa (P.R.P.).
Asalin wannan Gari na Iggi ya sami sunan sa daga wani bafulatani mai suna Iggi. Wanda duk shekara yana zuwa yana kiwo da Dabbobin sa a wannan wuri lokacin wannan wuri yana Daji. Daga baya sai wani Mutum mai suna Muhammadu mai gatari yazo shi da matarsa da yayansa hudu ya zauna a gindin wata Tsamiya ya kafa gidan sa. Muhammadu mai gatri shi ya sari wannan Gari wanda ake kira Iggi. Da garin ya fara bunkasa sai wani Mutum yazo mai suna Shuaibu ya zauna, wadda mutanen wannan Gari na Iggi sukayi shawarar yakamata a yiwa Shuaibu shugabancin Garin Iggi, kuma a yiwa ma’ajin baka shugabancin Daji, duk abinda ya shafi gari Shuaibu shine mai hukunci wanda ya shafi Daji kuma Ma’ajin Baka shine mai hukunci. Sakamakon Yake-yake da Iggi tayi Jama’ar garin suka yi shawarar cewa yakamata ayiwa Garin Ganuwa. Wannan gari na Iggi yayi Yake-yake da garuruwa da dama ciki akwai Ningi, wadda har kayan yakinsu an kwace daga hannun ningawa. Sarakunan da suka Sarauci Iggi Sune: - 1. Shu’aibu 2. Muhammadu Baleri 3. Abdulsalami Muhammadu Baleri 4. Sarkin Fulanin Durbunde 5. Mallam Talba 6. Umaru Talba 7. Abubakar Babur Abdulsalami I 8. Abubakar Abdulsalamu II 9. Muhammadu Jabuwa Abubakar Koni 10. Yusifu Muhammadu Jabuwa 11. Alhaji Muhammadu Adamu Abubakar II Ayanzu aka samu cigaba aka rabashi wannan gari na Iggi biyu aka yiwa dan uwan Digacin Iggi na Goma sha daya Sarauta, wadda ake kiran sa Digacin Dirbundawa mai Suna Ibrahim Adamu Abubakar II. Kuma Shine Magajin Garin Iggi. Gundumar Iggi nada Digatai Ashirin (20) kamar haka: - 1. Iggi 2. Arobade 3. Yalwan damai 4. Unguwar “Ya 5. Yarma 6. kawo 7. Warwade 8. Budusu 9. Karan Gaza 10. Kuntu Kallo 11. Kwarsawa 12. Durbundawa 13. Tudun Babbassa 14. Ramin Kura 15. Jan Biri 16. Dangolin 17. Farar Godiya 18. Rumbun Wuya 19. Dokoki 20. Jiboga An kafa garin Sindimina a shekara ta dubu daya da dari bakwai da goma sha takwas (1718). A kwai wani mutum maharbi mai suna Ayagi yataso daga garin Katanga ya biyo daji, a inda har ya kaiga wata katuwar kuka, daga nan sui ya nuna sha’awarsa ta ya zauna a wannan gindin kuka. A wannan lokaci ne maharbi Sarkrin baka Ayagi yaje garin Birni-kudu, a zamani Mallam Muhammadu Maje Gaya ne ke Sarauta domin neman izini agareshi da kuma neman amincewarsa. A lokacin Sarkin kudu ya saurari Ayagi tare da bukatumsa. Mallam Muhammadu Sarkin B/kudu, ya taso da kansa tare da fadawansa sun dunguma zuwa wannan jeji a inda shi Ayagi ya sauka domin ya nunawa Sarki Mallam Mahammadu Maje Gaya a lokaci nne bayan sun zagaya wannan jeji suka kuma karasa gindni katuwar kuka sai Sarkin ya shafa wannan katuwar kuka, a nan ne ya buda baki yace Sindimina, wannan shine asalin sunan da aka samu. A nan take yaba Maharbi Ayagi izinin zama a wannan guri. A wannan zamani ne mutane daga kasar Jama’are, a wani gari mai suna Zurara, da ake kiransu Barnawa suka bakunci wannan maharbi mai suna Ayagi. Asalin wadannan mutane Fulani ne, kuma suka cigaba da zama tare. A wannan lokaci a kwai suma rikuminsu suka kawo chaffa a wannan gari na Sindimina kuma suka zauna tare. Da mutane suka hadu da yawa shine sukayi shawarar ya kamata su sami shugabansu. A lokacin da suka Ziyarci Hakimin Birnin Kudu, shikuma ya nada “MADIBO” a matsayin Digacin Sindimina wadda ya shekara (30). Bayan sane sai Maje Banbal Wanda ya shekara Ashirin da Bakwai (27) Yana mulki. Daga nan sai Ali Maje Birni ya sami Shekara ashirin da daya (21yrs). Daga nan kuma sai Sarkin Sindimina Usman ya sami shekare talatin (30). Duk a wannan shugabanni da suka gabata, tarishi ya nuna a zamanin Sarki Mai saje anyi yaki da Ningawa a inda Sindimina taci Ningawa da yaki kuma suka koresu. Daga nanne sai Sarkin Alhaji Muhmmadu Adamu wanda ya sami shekara hamsin da tara (51) yana Digaci. Alhaji Muhammadu shine Hakimi na farko da mai Martaba Sarkin Dutse Alh. DR. NUHU MOHAMMADU SUNUSI ya daga darajarsa ya zuwa matsayin hakimi daga watan maris 23’ 2001 ya zuwa 27th ga watan mayu 2002 wadda a wannan lokaci ne Allah yayi masa rasuwa. Sakamakon daukaka darajarsa da Allah yayi masa, aka sami Karin Digatai guda biyu sune Sindimina kudu, wadda aka nada kaninsa Hakimi Sarkin yakin Dutse. Sunan wannan Digacin Sindimina kudu shine Mallam USMAN ADAMU A Matsayin magajin gari. Sannan sai shi ainishin dan maigirma marigayi Sarkin yaki a matayin Digacin Sindimina Arewa shine Adamu Muhammadu. Wannan Gunduma ta sundimina tana da Digatai kamar haka. 1. Sundimi kudu 2. Sundimia Arewa 3. Kumbura 4. Gargadi 5. Kwari 6. Safa 7. Nafara 8. China’a 9. Kadangare 10. Hirin 11. Nafada 12. Kwangwara Ainishin Sarautar da mai Martaba ya nada wannan MaSarauta itace ta Sarkin yakin Dutse. Bayan rasuwar Sarkin yakine aka nada Abdulkarim Iguda a matsayin Hakinin Sindimina a matsayin Sarautar FAGACIN DUTSE. A takaice tun kafin Jihadin Shehu Usman dan Fodio, anyi wani shahararren malami mai suna Mallam Isyaku, mahaifin Mallam Lawan (Wanda ya kafa Gwaram), Mallam Isiyaka waliyyin Allah, Malami kuma Bafillatani daga baya ya zama babban Almajirin Shehu Usman Danfodiyo. Mallam Isiyaka yana da Almajirai masu yawan gaske, daga cikinsu akwai Yakubu wanda mahaifansa duk warjawa ne, amma shi yakubu bashi da aiki sai karatun Alkur’ani da koyar da Addinin Muslunci. Lokacin da Shehu Dan Fodiyo ya bayyana sai Mallam Isyaku ya debi Almajiransa don ya kai masa caffa tare da Mallam Abdulsalamu wanda Allah ya hada zumuntarsu da mallam Isiyaku acan Sokoto. Har aka fara Jihadin jaddada Addinin Muslinci. Ganin haka Mallam Yakubu ya shawarci Mallam Isyaku da Mallam Abdulsalamu da suma su karbo Tuta a gun Shehu. Aka basu amma Mallam Isyakune ya karbi Tutar ya kuma umarci Abdulsalamu dasu tafi kasarsu don yin Jihadi tare, amma sai Abdulsalamu ya gayawa mallam Isyaku cewar za koma kasarsu, Auyo don jaddada Muslinci da alkawarin zasu rinka ziyartar junansu. Lokacin da Mallam Isyaku zai tafi, sai Shehu ya tambayeshi ko yana da Da? Sai yace A’a sai dai babban Almajirinsa, wato yakubu wanda ya auri babbar Yarsa. Su kai sallama da Shehu suka nufi shiyyar da Bauchi take a yanzu a dai dai wani gari mai suna Yalwan dan Ziyal, Allah yayiwa Mallam Isyaka rasuwa. Daganan sai yakubu ya koma ya bayyana masa abun da ya faru kuma ya nemi Shehu da ya aikawa abdulsalamu aminin Mallam ya dawo ya shugabancesu. Amma sai Shehu ya umarceshi daya tafi ya shigar da mutane Addinin Muslinci. Bayan ya dawo ya sami Jama’arsu harda Lawan dan Mallam Isyaku yayi musu bayani cewa Shehu ya umarceshi daya rike Tutar amma Mallam Lawan yace Tuta ta Ubansace, kuma Shehu yace bayan shekara daya za’a dinga amfani da ita. Mallam Lawan ya Umarci Yakubu daya rike Tutar har sai da shekara tayi sai ya cira tutar, jin labarin wannan tuta yasa arna suka rika karya Kwari da bakansu suna shiga Muslinci, cikin wani karamin lokaci Yakubu ya sami mutane masu yawan gaske suka kama addini Muslinci. Ganin wannan nasara tasa Mallam Lawan ya bukaci Yakubu daya bashi Tuta amma Yakubu yaki bashi. Saboda haka Mallam Lawan ya taso daga cikinsu ya koma wani gari da ake kira Ganjuwa kan hanyarsu kafin su kafa Gwaram, daga nan Mallam Lawan yayi fushi yatafi gun Shehu ya bayyana masa yaga wani waje wanda yake tsakanin Katagun da Bauci ana kiran wurin Kijin don ya zauna da Jama’arsa, sai Shehu ya hada shi da Liman Dabo daya daga cikin Almajiransa, wanda yake Kano a wancan lokaci. Saboda baiwar da Allah yayi wa Mallam Lawan, Liman dabo yace zai raba Kano biyu ya bashi rabi amma sai shi Mallam yace a’a yafison Kijin. Mai karatu zaiso yaji yadda rabuwar mallam Lawan da Mallam Yakubu ta Kasance shi kuma ya kafa Kijin kafin Gwaram. Lokacin da Mallam Lawan ya Kijin ya Iske wasu kabilu ana kiransu Janganawa, wasu arna da basu da aiki sai Noma da farauta, yai musu sallama yace musu “Dinmoi” sannan yace musu “dingarko” wato bakone, sukai maraba dashi suka tarbeshi suka bashi Masauki. Ana cikin wannan hali sa Mallam Abdulsalamu daga Auyo shida mutanensa, dai-dai lokacin da suke fada da Buhari ya sami labarin rasuwar Mallam yazo ta’aziyya daga nan sai Mallam Abdulsalami ya umarci Mallam Lawan dasu tashi daga nan su koma gindin wani Dutse wato gurbin da Gwaram take a yanzu domin yafi fili ba komai a gurin sai shinge na Joganawa wanda suke Nomawa. Kafin su tashi su koma wurin da Gwaram take, sun zauna a Kyauran gana wanda mutanen da aka samu awurin su Malamai ne. sune Gidan malami na yanzu, kamar kilomita biyu kudu maso yamma da masaukinsa na farko. GWARAM KARKASHIN KASAR KANO Gwaram wadda take kilomita 190(Km) daga kudu maso gabashin Kano, nanne fadar mulki ta Gwaram, wannan gari yana daya daga cikin manyan garuruwan Kano, tun lokaci mai tsawo daya gabata in banda Gaya da Jahun wanada suka riga Gwaram kafuwa. Gwaram tanada dogon tarihi wanda ya hade da Jihadin Shehu Usman Danfodiyo 1800AD. A wannan wuri da garin gwram take a yanzu dacan akwai wata kabila da suka zauna a wurin ana kiransu Janganawa wanda suke masu karfine kwarai da gaske, tarihi ya nuna suna zaune a wani wuri daf da kogin Gwaram ana kiran gun Kijin, saboda haka ma ake cewa asalin mutanen Gwaram Janganawa ne. A wannan guri da suka koma basu tarar da kowa ba sai wani kasurgumin maharbi mai suna Gware, shi wannan Mutum ya shahara baya bukatar wani ya matsa masa a wajen zama don haka ganin Mallam Lawan yazo kusa dashi yana kuma koyarwa sai yayi shijira ya bar gun wannan shine karshen barinsa gindin Dutsen. Daga nan sai Mallam Lawan ya mike kafa sosai yana Karantarwa bisa umarnin Shehu. Garin Gwaram ya far hada Jama’a ta Ko’ina, da suka kawo caffa irin su Auyakawa, daga Auyo, Hadejia, Agalawa, Bare-bari da Warjawa daga kasar Bauchi bayan daular muslinci ta fara haduwa daga baya aka canjawa Gware suna zuwa Gwaram kamr yadda Jikar ta koma Jikas. Wannan gari yanada gidajen Sarauta Uku (3), Gidan Mallam lawan, Gidan Yarima Musa da Gidan Mamman babban wurin da Hakimi yake wato masallacin Juma’a na yanzu.Gwaram ta yanzu da akewa kirari “Ta Mallam Lawan da Musa mai hayakin Kudi ko ta musa Ilorin Gabas” ta shahara tun kafin 1800AD. Tana da Digatai**** masu Unguwanni***** DALILAN RUSHEWAR SARUTAR GARGAJIYA TA GWARAM Akwai dalilai masu dama wadanda suka sa Sarautar Gargajiya ta Gwaram ta rushe. Hakan tafaru ne a lokacin Sarkin Gwaram Ali dan Musa (Maina Bawa), amma sahihin bayani shine Turu abinda ake nufi da Turu shine Tawaye ko Fitina ko kin bin umarni, wato sarakunan mu na wannan lokacin sun yiwa Sarkin Kano Turu ne. Koda yake Ruwa baya tsami banza idan kaji gudu da labari, abinda ya kawo wannan Turu a shekarar 1917-1918 shine karyewar kudin haraji ko kudin kasa da Jangali a wancan lokaci a hannun Sarkin Gwaram Maina Bawa. Karyewar wannan kudin kasa ya faru sanadiyyar zuwan Sarkin Kano Muhammadu Bello bikin bude ko bada izinin karbar kudin Haraji da Jangali na wancan lokacin inda Sarki yayiwa Sarki da Jama’arsa hidima, bayan an kammala tara kudin kasa sai ya kai kudi bai cika ba ba fan Talatin aka umarceshi in cikon ya samu ya kawo. Bayan wani lokaci sai Sarkin Kano ya aiko Madaki azo a karbi sauran kudin a wurin Sarkin Gwaram in da ya nuna sai an bashi koda karfine, inda nan take yace baza’a biya wannan kudi ba don kuwa an yiwa mutanensu hidima ne, madaki ya koma ya fadawa Sarkin Kano wannan labari inda Sarki ya fusata yasa a kira masa Sarkin Gwaram koda Sarkin Gwaram yazo sai Sarkin kano ya Tambayeshi ya maimaita masa abin da ya fadawa Madaki wannan tasa Sarki ya harzuka ya umarci Sarkin Gwaram daya dawo ya bada wannan kudi kokuma abakin Rawaninsa. Bayan wani lokaci kudin basu samu ba sai Sarkin Kano ya tubeshi yayi masa murabus aka nada Sarkin Dawaki Idris aka turoshi Gwaram a mukamin Hakimi a (1918 – 1920) har yanzu1997 ake nada Hakimai ake turawa Gwaram anyi hakmai Ashirin da Daya (21) kamar haka: - 1. Sarkin Dawakin Kano Idrisu 1908 – 1910 2. Sarkin Dawakin KanoAbdullahi 1910 – 1916 3. Sarkin Dawakin Kano Isa 1916 – 1920 4. Sarkin Dawakin Kano Amadu 1920 – 1922 5. Sarkin Dawakin Kano Muhammad 1922 – 1925 6. Sarkin Dawakin Kano Abubakar 1925 – 1942 7. Magajin Mallam Kano Sani 1942 – 1948 8. Dan Buran din Kano Faruku 1948 – 1955 9. Barden Kano Habibu 1955 – 1958 10. Barden Kano Bashari 1958 – 1960 11. BardenKano Ibrahim I 1960 – 1963 12. Dan Amar Kano Hamidu Bayero 1963 – 1968 13. Barden Kano Ibrahim II 1968 – 1971 14. Magajin Mallam din Kano Abdullahi 1971 – 1974 15. Matawallen Kano Ibrahim 1974 – 1977 16. Gado da masun Kano (Wakili Ado) Habibu 1977 – 1979 17. Tafidan Kano Mahmood Usman 1980 – 1983 18. Sarkin Dawakin tsakar Gidan Kano Isa 1983 – 1985 19. Dan Makwayon Kano Abdullahi Aminu 1985 – 1995 20. Dan Lawan din Kano Garba Abbas 1995 – 2000 21. Turakin Dutse Bello Basiru 2000*** Karamar Hukumar Gwaram na alfahari da wadannan ‘ya’ya nata: - 1. Alhaji Halluru Abubakar Gwaram – Tsohon Malamin Makaranta bidan fari kuma Malamin Hakimin Chamo. 2. Alhaji Umaru Zandam – Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa kuma Kwamishina a Ma’aikatar daukan Ma’aikata ta Jihar Jigawa. 3. Alhaji Bello Maitama – Tsohon Ministan Ciniki a Tarayyar Nigeria a Jamhuriya ta biyu (2), dan Majalissar Dattijai mai Wakiltar Jigawa ta Tsakiya kuma Sardaunan Dutse. 4. Alhaji Tijjani Abubakar – Tsohon Mai-Sharia a Jihar Kano kuma Shugaban masu Sharia a jihar Jigawa. 5. Alhaji Ahmad Hassan Kila – Shahararren dan Kasuwa. 6. Alhaji Isyaku Farin Dutse – Tsohon Ma’aikacin Ma’aikatar Ilmi kuma Kansila a Karamar Hukumar Gwaram. 7. Alhaji Tukur Fagam – Tsohon Malamin Makaranta kuma dan Majalissar Tarayya a Karamar Hukumar Gwaram. 8. Alhaji Abubakar Tsangarwa – Tsohon Darekta a Ma’aikatar kasa da Safiyo ta Jihar Jigawa. 9. Alhaji Ibrahim Basirka – Tsohon Sakataren Karamar Hukumar Kiyawa. Garin Fagam dayake kudu da gwaram ta yau wurine mai tsohon tarihi. Mazauna farko suna daga cikin rundunar Bayajidda lokacin daya taho daga Borno kan hanyarsa ta ta Gabas zuwa Daura. Wannan Mutane maharbanedan haka da suka zo Duwatsun hira sai suka dan tsaya saboda ganin wurin mai Daji da namun Dajine.suka kafa garin da ake kira KULIN FARDI. Daga cikinsu wani da ake kira Muhammadu Aifama da Dansa Jurin tare da ‘yan uwansa suka sake yin kudu da Shira ta bangaren wani tsauni yamma da Gadama da ake kira HAWAN DAWAKI. JURIN daya shahara sai ubansa ya nadashi Sarkin Bakar Shira don ya kare musu kudu saboda farmakin da Sarkin ganjuwa ta Bauchi yake kawomusu. Wasu mutane biyu (2) ganin shahararsagashi kuma mahaifinsa ya rasu sai suka zuga shi ya kafa garinsa maimakon zama karkashin Sarkin Shira. Ya yarda ya kafa Garin LAKWATI da yayiwa ganuwa da kofofi goma sha biyu, Duwatsun Shira, Ganjuwa, da Dutsen Kila. Don haka ya shiga cin gashin kansa, kuma suka shiga zamansu lafiya dashi da ‘ya’yansa (4) a cikinsu a kwai Gagarau, Nakauda, Chulatuwayi da autansu Muhammadu Abasawa. Jurin ya fadada kasarsa daga Gabas saida yayi iyaka da Misau ta Yamma yayi Iyaka da Ganjuwa da Shira. Wannan wurare da yayi Karin shi ake kira “ASA”. Shugabannin garin Fagam kamar yadda za’aga a gaba sun shahara kuma sunyi Yake – yake na sara da suka zamuga yadda suke a ayau. Jurin yana kan shahararsa sai ya sami labarin tahowar wani Malami Sarki waishi Mallam Zaki, daya bullo daga garin Yayun ta kasar Shira a wancan zamanin. Jarun ya kaiwa Mallam Zaki farmaki, amma kafin Jurin yakai shi kuwa Mallam zaki ya gudu Gwaram ya buya amma saida Jurin yaywa Gwaram Kawanya ya kuma sauka a bakin Kogin ya tsare inda mutanen Gwaram suke shan Ruwa har kwana tara (9). Wannan yasa mutanen Gwaram da daddare suke tona Rijiya don su samu ruwan sha. Bayan Jurin ya tashi sai Mallam Zaki ya tafi yayi tafiyarsa Gudiri yayi Hijira 1780. Tasowar Jurin da Jama’arsa suka kama sabon Garin da yake tsakanin gindin Duwatsu. Inda suka samu wani Mutum mai suna Fagam. Wanda garin Fagam ya samu sunan daga gareshi, kuma ya haka wata Rijiya da ake kira SHALIN har yanzu mutanen Fagam suna shan ruwan wannan Rijiya. Jurin baibi abokinsa yakubu Bauchi. Kuma Yakubu ya shaidawa Shehu cewa tsufa ya hanashi zuwa amma ga dansa ya baka amana. Shima Shehu Usman Danfodiyo ya barwa yakubun Bauchi amanar Muhammadu Abar – sama amana wadda daga karshe yakubu ya aurarwa da Muhammadu Abar-sam ‘yarsa ya turashi Darazau ya tare masa hare-hare. Daga baya Jurin ya rasu a 1802AD. Kuma dansa MAKANDA ya gajeshi a shekara ta 1825. shima yabi ubansa Muhammadu, Fagam ta zama ba shugaba. Ibarahim Nahana ya gajeshi ya zama Sarki na hudu dukka ba’a jituwa da MaSarautar Kano, Ibrahim Nahana ya aikawa Sarkin Kano ya turo masa wani Malami ya koyar dasu Addinin Muslinci. Sarkin kano ya turo Mallam Dalha bisa wannan bukata. Sarki Ibrahim ya zama adali kuma Fagam taci gaba a lokacinsa. Wani lokaci abubuwa sukan yi zafi da wannan yahau sai wannan ya ture sh, har akazo lokacin da Danyaya yayi amfani da mutane ya yaki Fagam ya nada nasa Sarkin. A wannan lokaci sha’ani yayi tsauri Fagam ta zama cikin mawuyacin hali. Har takai wani Jarumi mai suna GALAMI Sarkin Kudu ta Kano ya hari Sarkin kano Alu ya turashi don ya daidaita garin. Zuwan wannan Mutum sai Mutanen Fagam suka hade kansu suka ki bin galami wannan yasa yabar kasar. Amma dansa BAGGU kafin ya bishi ya mulki Fagam na dan Tsawon lokaci. Shima ya tafi. Fagam ta zama ba shugaba. Wannan hali yasa Sarkin Kano Alu da kansa cikin shekara ta 1902 yazo yaga halin da Fagam take ciki. Dayazo ya tara Sarakunan Woso, Bauchi, Kwarko da Galambi don ayi musu Sulhu amma abin bai yiyuba, wasu daga cikinsu suka hada kai da Sarkin Ningi yazo yacisu da Yaki. A shekara ta 1902 aka nada Sulaimanu wandara Sarkin Fagam, a shekara ta 1903 sukaci kano da yaki, fagam taci gaba da zama karkashin Kano. Daga nan aka daina aikowa da jakadan Sarkin Kano. Fagam ta koma karkashin Gwaram. A lokacin Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi aka bawa Fagam Sarautar Hakimi, aka bata Gunduma ranar 7 ga watan Augusta, 1999. bayan anyi wakili Alhaji Ahmad Badayi Falakin Dutse, aka nada Alhaji Muhammadu Yayari Sarautar Shatima kuma Hakimin Fagam ranar 16 ga watan Feburairu, 2000. WADANDA SUKA MULKI FAGAM A MATSAYIN HAKIMI 1. Alhaji Ahmad Badayi Falakin Dutse – 7 ga watan Agusta, 1999 – 16 faburairu, 2000. 2. Alhaji Garba Muhammadu yayari – 16 ga watan Fabrairu, 2000 – 2003. 3. Alhaji Adamu Idris Katukan Dutse 2003 - …… Gundumar Fagam tanada Digatai 23. 1. Fagam 2. Haya 3. Kwarko 4. Nassarawa 5. Tsakuwarau 6. Farin Dutse 7. Ganji 8. Dangulan 9. Lafiya 10. Shari Hori 11. Gadama 12. Bango 13. Kalasu 14. Galambi 15. Yarfi 16. Dingaya 17. Hawan Doko 18. Kilawa 19. Bagadaza 20. Laya 21. Jingino 22. Jaryata 23. Gwani GUNDUMAR JAHUN Kasar Jahun dai tana gabas maso Kudu da Kano, Kuma gabas maso Arewa da garin Dutse. Mutanen kasar YAWANCINSU Fulani ne da Hausawa da kuma Barebari kadan. Sana’ar mutanen kasar Kiwo da Noma, amma mutanen Arewacin kasar suna noman rani da kuma Kifi (SU) sabo da Allah ya albarkaci yankin da ruwa, harma ana kiran jama’ar yankin kwarawa. KAFA GARIN JAHUN Gurbin da garin Jahun yake a halin yanzu da can kun- gurumin jeji ne da Allah ya yiwa albarkar Fadama da kuma namun jeji masu tarin yawa. Ance tun kamar shekara ta 800 AD wani Bamaguje mai suna JANZAKI yazo daga Auyo da ‘ya ‘yansa HADE-DA-JIYA ya kafa garin Jahun. Wata fadar kuma tace shi dai JAN-ZAKI yana daga zuri’ar KIGO ne wanda ya zauna a jejin Miga. Kuma yazo ne da Matarsa da ‘ya‘yansa biyu (1) HURTIMI (2) BAWADA. Kuma ya zauna a kusa da daya daga Fadamun jejin da ake kira FAGEN KURA nan Arewa da inda Jahun take a yanzu. Ance shi dai Janzaki yayi nisan kwana yasamu kamar shekara dari (100) a duniya.Bayan Janzaki ya rasu sai Hurtimi ya gaje shi a matsayin shugaba. Shi kuma ya zauna a gabas da tsohuwar sakatariya. Bayan rasuwar Hurtimi sai Kaninsa Bawada ya gajeshi. Shi kuma ya zauna a inda Asibiti yake a halin yanzu a kusa da wata bishiyar kuka da ake ce mata kukar BAWADA. Shima dai ba’a san yawan shekaraunsa ba. JAHUNO Bayan rasuwar Bawada a shekara ta 1600 AD. Sai wasu Fulani su biyar (5) Daga kasar MALI suka fito da shanunsu kamar dubu biyar (5,000). Wadannan Fulani sune:-1. JAHUNO 2. SHANO 3. BEBE 4. GWARKO 5. DARKIDO Wadannan Fulani sun shigo Nigeria ta kasar Katsina, suka biyo ta Gwarzo, da suka iso wani bakin Rafi da ake ce dashi MARASHI sai shano ya zauna anan, shine ake kiran wajen Shanono. ‘Yan uwansa hudu suka wuce suka yi kudu har zuwa inda Bebeji take a yanzu sai shi kuma BEBE ya zauna anan, shine ake Kira Bebeji. Sauran suka wuce zuwa inda garin Garko yake a halin yanzu inda shi kuma GWARKO ya zauna a ke kiran garin Garko. Jahuno babbansu da kaninsa Darkido suka yi gaba kadan ya zuwa inda Darki take a yanzu, a inda shima Darkido ya zauna daga nan sai Jahuno ya wuce har bakin wata Fadama a nan kofar inda Jahun take a yanzu ana kiran Fadamar AKAMA inda ya iskewasu maguzawa suna sassakar Ganguna da Akusa, shima saiya sauka anan ya zauna tare dasu. Saboda Jahuno yazo da dukiya mai yawa da shanu masu yawan gaske sai suke girmamashi, suka mayar dashi kamar shugabansu, ya iso wurin a shekara ta 1600 AD. Bayan kamar shekara biyu, (2) da zuwansa ya basu shawarar cewa bai kamata su zauna hakaba, saboda haka ya kamata su kai Caffa gurin Sarkin Kano dan kada azo a mamayesu da yaki. Maguzawan suka yarda, suka tafi da shanu da dukiya mai-yawa suka kai caffa wajen Sarkin Kano na wanna lokacin. Nan take Sarkin Kano Jahuno (ARDO) ya zama ARDO JAHUNO a shekara 1800 AD daga nan garin Jahun ya samo sunan sa. Ardo Jahuno shine na daya daga manyan Ardo din Sarkin Kano, sabo da biyayyarsa da yawan dukiyarsa, ya kuma mallaki Jama’arsa kwarai da gaske. MULKI DA DANGANTAKA Bayan rasuwar Ardo Jahuno wato Sarkin Jahun, zuriyarsa sunci gaba da mulki a masarautar Jahun har zuwa wannan lokacin. A cikin lokutan wannan mukli ne Sarkin Kano Abdullahi B. Ibrahim (1855) ya baiwa wasu daga Sarakunan kasarsa auren ‘ya ‘yansa da kannen sa, dan a kara dankon zumunci da kuma shigo dasu harkokin mulki. Sarakunan da aka baiwa auren matan sune:- Sarkin Jahun, Sarkin Dutse, Rano da Kura. An baiwa Sarkin Jahun ‘Yar Sarkin Kano mai suna Rabi. A shekara ta 1882 Jahun da Dutse sun zama dangi Sullubawan Kano ta auratayya a tsakaninsu.Bayan rasuwar Sarkin Kano Abdullahi B. Ibrahim sai Kaninsa wanda suke ciki daya Muhammadu Bello yahau karagar mulki. Sarki Muhammadu Bello yaba duk Sarakunan sa auren ‘ya ‘yan Sarki ko kannensu su sakko su kuma bar sarautarsu. Wasu daga cikinsu sun bi doka a inda abin da suke gudu ya faru a kansu na barin sarautar. Sarkin Jahun yana daga wanda suka ki bin wannan umarni, ya kuma ki barin sarauta. A wannan lokaci Sarkin Jahun yana takama da Mayaka da Dakaru sama da dubu (1000) kuma shine mai karewa Kano a yaki inya bullo daga Gabas, harma ana kiransa kyauren gabas. Sarkin Jahun na lokaci shine Moddibo (kalmar da take nufin Malam ko masani a Fulatanci) shi Maddibo dane ga Sarkin Jahun Sarkiyo, Jika ga Sarkin Jahun Maje gabas. Sarkin Jahun Maddibo YA shahara sosai wajen yake-yake da kuma karfin iko akan Jahunawa a duk inda suke inda yake ikirarin duk Bafulatani mai jar-saniya talakansa ne a duk inda yake, kuma turawa a karbo masa Jangali a gusa.Bayan Sarkin Jahun Ardo Jahuno anyi Sarakunan Fulani da dama kafin a aiko da Hakimi daga Kano. Sarakunan Fulani da suka mulki Jahun daga farko ya zuwa yau sune kamar haka:-SARAKUNAN FULANI JAHUN:-
Ana cikin wannan mulki na Fulani a Jahun sai Sarkin Kano da Hakimi Barde Abdullahi na Gwangwazo a shekara ta 1908 AD. Ga sunayen Hakimin Jahun Daga zuwan Barde Abdullahi1. Barde Abdullahi Na Gwangwazo 1908 – 19172. Barde Lamido 1917 –19233. Barde Sama’ila 1923 – 19394. Dan Makwayo Yusifu 1939 – 19485. Dan Amar Yusif 1948 – 19496. Magajin Malam Muhd. Sani 1949 – 19537. Dan Lawan Ibrahim 1953 – 19628. Sarkin Dawaki Isah Abbas 1962 – 19679. Turakin Kano Maje Abdullahi 1967 – 197610. Dan Lawan Bashari 1976 – 197711. Sarkin Dawaki Bello Dan dago 1977 – 197912. Bauran Kano Tata Galadima 1979 – 193313. Dan makwayo Bashari 1983 – 198414. Baura Abdullahi Mai kano 1986 – 199215. Blarabe Ahmed (Magajin Rafi) 1993 – -WAKILI Awani lokaci an samu wakilai da akan tura duk lokacin da hakan ta taso. Wadanda su kayi wakili a Jahun sune:-1. Shehu dogari 2. Najalo 3. Gwadabe 4. Sarkin Malfa 5. Namadi 6. Inuwa 7. Ado Odile 8. Sarkin Dogaran Dutse 9. Sarkin Bakin Dutse GUNDUMAR JAHUN KARKASHIN MASARAUTAR DUTSE Gundumar Jahun ta koma karkashin mulkin Masarautar Dutse a shekara ta 1991 a lokacin da gwamnatin tarayya ta kirkiro Jihar Jigawa alokacin Mulkin Marigayi Sarkin Dutse Alh. Muhammadu Sunusi wanda bayan rasuwarsa Alhaji Muhammadu Nuhu Sunusi ya gajeshi. Wannan Karamar Hukuma ta kunshi Gundumomin Jahun, Aujara, da Gunka. Kuma tana alfahari da wadannan ‘ya’ya nata: - 1. Dr. Ishaku Malami a Jami’ar Bayero kuma Sakataren kungiyar cigaban MaSarautar Dutse. 2. Alhaji Sulaiman Jahun – Tsohon kwamishinan Shari’a na Jihar Kano. 3. Alhaji Habu Gwari – Tsohon Shugaban Karamar hukumar Jahun na farko. 4. Alhaji Baffa Aujara – Tsohon Malamin Makaranta kuma Sakataren Ilmin Karamar Hukumar Kiyawa. 5. Alhaji Idi Aujara – Tsohon malamin Makaranta kuma babban sakatare a ma’aikatu daban – daban a Jihar Jigawa. 6. Alhaji Bala Safiyanu Jahun – Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Jahun, Tsohon mai baiwa Gwamna shawara kan raya Karkara, Tsohon mai rikon mukamin Gwamnan Jihar Jigawa, kuma mai baiwa Gwamnan Jihar Jigawa Shawara kan Tsaro. 7. Alhaji Babannan Rabo Aujara – Tsohon Shugaban Majalissar Jihar Jigawa, Kwamishinan Lafiya kuma kwamishinan Ma’aikatar Addini ta Jihar Jigawa.
Aujara tsohon garine kuma ya sami sunansa daga wani tsohon Mutum mai suna Kado Aujare wanda yazauna a wurin tare da Shanunsa da Dukiyarsa. Daga baya wadansu mutane suka taso daga wani gari mai suna Gabasawa suka hadu da Jama’ar Kado Aujare sannan ne aka saka wa wannan gari suna AUJARA. Gundumar Aujara kasa ce mai albarka wajen Noma, Kiwo saboda haka mafi yawan mazauna kasar Manomane. A cikin ‘yan shekarun baya babban abinda gundumar ta shahara dashi shine Noman Gyada da Shinkafa. A yanzu haka da Dawa, Ridi da Rogo sune abubuwan da Mutanen suka fi nomawa. Haka kuma gundumar ta shahara wajen sana’oi kamar su Kira, Rini, Sassaka, Saka da sauransu. Shekara aru – aru da suka wuce (har zuwa 1975) Aujara kasar Digaci ce akarkashin Sarki ko Hakimin Jahun. Amma a sakamakon sabon tsarin kananan hukumomi da aka samu a wancan lokaci Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya maida wannan Gari mai dinbin tarihi MaSarautar Hakimi ya sanya Digatai ashirin da shida(26) a karkashinta Kabilu biyu suka mulki garin aujara, Habe(wato Hausawa) da kuma Fulani a mukamin Digatai HABE SUNE KAMAR HAKA: - 1. Bawada 2. Abdullahi 3. Watuwo Ranau 4. Abdul D/ Watuwo Ranau 5. Saddi D/ Watuwo Ranau 6. Bako Hassan 7. Yusufu Gaddi 8. Bako Hassan 9. Galadima Bako FULANI SUNE KAMAR HAKA: - 1. Mahammadu Jata 1806 – 1821 (15) 2. Gayya Muhammadu 1821 – 1838 (17) 3. Kartaji Gayya 1838 – 1844 (6) 4. Salihu Tajo 1844 – 1865 (21) 5. Ibrahim Salihu 1865 – 1883 (18) 6. Mamman Ibrahim 1833 – 1908 (25) 7. Hamidu Modibo 1908 – 1949 (41) 8. Alh. Usman Hamidu 1949 – 1979 (21) 9. Alh. Hassan Hamidu 1970 – 1989 (18) 10. Alh. Bashir Ahmad 1989 – 2001 (12) 11. Mustapha Bashir 2001 - …… 12. Bilyaminu Hassan 2001 - ……… Sakamakon amincewar da mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu Muhammadu Sanusi ya samu daga zababben Gwamnan Jiha Alhaji Ibrahim Saminu Turaki akan Karin Gundumomi a cikin shekara ta 2001 wadda sakamakon hakane Sarkin Aujara na wannan lokaci Alhaji Bashir Ahmed kuma sarkin Fulani na goma (10) daga cikin sarakunan Fulani ya sami cigaba aka bashi mukamin sarkin Yamman Dutse sannan kuma aka turashi wata sabuwar gunduma a kasar Birnin kudu da ake kira Wurno Samun wannan cigaba nasa yasa aka raba garin Aujara zuwa kashi biyu (2) wato aka nada Digatai guda byu aciknsa. Digatan da akayi sune: - 1. Mustapha Bashir wadda akayiwa magajin Gari mai kula da kudu da Gari 2. Bilyaminu Hassan wadda aka yiwa sarkin Arewa mai kula da Arewa da gari Wannan kari na gundumomi ya jawo anyi wata sabuwar gunduma daga cikin Gundumar Aujara da aka kara da sunan gundumar Gunka a shekara ta 2001. Kirkiro wannan gunduma ta Gunka yasa aka kwashe wadansu garuruwan dagatai guda tara(9) wadda ake kira Hayin tara daga jikin Aujara. Kuma Gundumar aujara tana da garuruwan Digatai (26) Ashirin da shida kamar haka: - 1. Magajin Gari 2. Atawane 3. Sarkin Arewa 4. Kanawa 5. Takuyawa 6. Damutawa 7. H/Tsohuwa 8. Gaure 9. H/Sabuwa 10. Gadewa 11. Garado 12. Kuka Kwance 13. Garan 14. Afasha 15. Gabari 16. Gaskawa 17. Laraba 18. Nahuce 19. Jabarma 20. Taraya 21. Magama 22 .Zarge 23. Atuman 24. Tunobo 25. Dina 26. Kargo Kamar yadda akaga bayani abaya cewar an sami tsohuwar Gundumar Aujara a 1976 a wannan lokaci ba’a kirkiro Jihar Jigawa ta yanzu ba don haka muna karkashin tsohuwar Jihar Kano tada, kuma mai Martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero shine yake turo Hakimai, ya turo Alhaji Muktari Zakari da mukaminDallatu kuma Hakimin Aujara na farko. A wannan lokaci Alhaji Garba Abbas Dan Lawan ya sami tarihi guda biyu, wato shine Hakimi na karshe da aka turo daga Kano haka kuma shine Hakimi na farko da aka turo a wannan Gari kasancewar a lokacinsane aka sami Jihar Jigawa ashekara ta 1991. Dan-lawan yana nan zaune a Aujara akayi masa canji zuwa Gwaram shi kuma Hakimin Gwaram na wancan zamanin wato Alhaji sarki Aminu Dan Makwayo wadda yake shima mutumin Kano ne sai yaki amincewa da wannan canji ya tattara kayansa ya koma gida wato Kano yaki zuwa Aujara, shi kuwa dan lawan ya tafi Gwaram. Wannan shi yasa aka kawo Kilishin Sutse a matsayin Wakilin Sarkin Garin Aujara, ya zauna har tsawon shekara biyu ba, a nada Hakimi a garin ba. WADANDA SUKAYI SARAUTAR HAKIMCI A GUNDUMAR AUJARA SUNE
Garin Gunka yasami sunansa daga wani Gunkin wasu Maharba Mallam Garba da kaninsa Mallam Abdu da suka zo daga Gaya. Wadannan Maharba sukan rataya kayansa a jikin wannan Gunki duk sanda zasu tafi farauta. Wannan yasa ake kiran wannan Gunki Gunka. Wannan Gunduma ta Gunka ta riga Gundumar Jahun kafuwa saboda Sarkin Kano mai Kutumbi ya fara nada Mallam Garba ya zama Digaci na farko Kafin tazama Gunduma. Gunka Garine da yake kewaye da Ruwa. Daga kudu duddurune ya shatata daga Arewa kogin Hadejiya ne ya zagaya ta, wannan yasa tana da wahalar shiga a Rani da Damina kuma shine dalilin da yasa aka amince da Hakimin Gunka na farko Barden Kano ya komo Jahun da zama. Kuma dama tun asali gunka karkashin Dutse take. Tsohuwar cibiyar cibiyar Gunduma daga Gunka zuwa Jahun sai ta koma matsayinta na Digaci. A shekara ta 2001 mai Martaba Sarkin Dutse, ya sake mata Hakimi Alhaji sale Ciroma, Sarkin fadar Dutse kuma ta koma gunduma karkashin Karamar hukumar Jahun. Gunka a wannan lokaci tanada Digatai Goma Sha daya (11) karkashin sabon hakiminta Alhaji Muhammadu Bauran Dutse. Garuruwan Digatan Sune: - 1. Gunka 2. Dari 3. Kale 4. Bura-buri 5. Doro 6. Gidan datti 7. G/Dango 8. G/Zaki 9. Oyaliman 10. G/Gona Garin Miga tsohon garine da aka dade da kafashi. Ana yiwa garin kira da mutumin daya kafashi wato Miga ta Kigo. Kigo wani shahararren Mutum ne wanda akan hanyarsa ta tafiyaFaranshi yaga gurin da daji da fadama sai yayi tunanin bari yazauna a Miga tare da iyalinsa. Wannan zama nasa ya ja hankalin Jama’a suka taso daga kusa da miga suka taru gu daya dashi. Yawancin mutanen Miga sana’arsu Noma da farauta daga baya suka shiga sana’ar sun Kifi. Ganin taruwarsu wuri daya sai suka amince da kigo ya zama shugabansu. Wannan tasa ya zama Sarkin Miga na farko daga cikin habe kuma masu mulkin Miga kuma masu mulkin miga daga na farko har zuwa na goma (10) duk zuriar kigone. Daga baya da aka sami wata yar matsala da tasa aka karbe garuruwan Miga itama aka maida ita Digaci kuma duk aka maidasu karkashin Hakimin Jahun, wannan yasa Fulani suka sami damar shugabantar mutanen Miga don haka daga Sarki na goma sha daya suka zama Fulanine. Sarakunan Miga Habe sune: - 1. Sarki Kigo yayi shekara 46 yana mulki 2. Mohd Bashar Dankigo yayi shekara 50 yana mulki 3. Sarki Tukulili yayi shekara 45 yana mulki 4. Sarki M. Dan-guru yayi shekara 50 yana mulki 5. Sarki Muhammadu Hamisu yayi shekara 39 yana mulki 6. Abubakar Hamisu yayi shekara 40 yana mulki 7. Sarki Muhammadu yayi shekara 40 yana mulki 8. S. Tukulili Abubakar II yayi shekara 30 yana mulki 9. S.M. Adamu dan Mohd yayi shekara 46 yana mulki 10. S. Mohd Tukulili yayi shekara 36 yana mulki 11. Ardo Jibago Dan Rabiu yayi shekara 11 yana mulki 12. Isah Jibago yayi shekara 42 yana mulki 13. Sarki Zakara yayi shekara 37 yana mulki 14. Mohd dan Isa yayi shekara 32 yana mulki 15. Abubakar dan mohd yayi shekara 44 yana mulki 16. Sulaiman Mohd yayi shekara 38 yana mulki 17. Abubakar Sulaiman yayi shekar 19 yana mulki 18. Muhammad Abubakar Wannan Karamar Hukuma data Kunshi Gundumomin Miga da Zareku na alfahari da wadannan ‘ya’ya nata 1. Marigayi Sarkin Miga – daya fito da miga ta hanyar aikin Gona tun lokacin Audu Bako. 2. Alhaji Sa’idu miga – Tsohon mai bawa Gwamnan Jihar Jigawa shawara kuma dan Majalissar tarayyar Nigeria. 3. Alhaji Abdulmumini Hassan Zareku – Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Miga sau Biyu (2). Alhaji Sabo Dan-Gyatum – Tsohon ma’aikacin gwamnati kuma dan kasuwa da yayi fuce a wajen samarwa Jama’a Ruwan sha. Garin zareku tsohon garine da tarihinsa ya fara tun wajen shekara 1500AD. Wato sama da shekara dari biyar (500) da suka wuce. Tarihin sunan garin da farko ance wani Mutum ne dayazo daga Rimi ta kasar Sumailan Jihar Kano da shanunsa zaiyi bayi da yaga wani Gulbi kan hanyar wucewar Turawa yan kasuwa sai yazamo yasawa gulbin suna Dagazo. Lokacin da turawan suka taho daga harbo suka tambayi shi wannan Mutum sunan garin don su sashi a taswira ya fada musu sunan garin Dagazo. Amma dai duk an yarda da cewa asalin sunan zareku ya farune daga kalmar Fulatanci Jireku da take nufin Kasar Nama. Saboda garin an yarada yana da wurin nama ga kuma gulbin da aka fara sawa suna garin watau Dagazo. Tun farko Fulani ke mulkin Zareku har zuwa yau. A cikin shekara ta 2001 mai Martaba Sarkin Dutse ya tabbatar da sabuwar gundumar zareku da aka cirota daga gundumar Miga. Hakimin farko da aka fara turawa Zareku shine Alhaji faruk Ahmad Wangara Madakin Dutse. Digatan Gundumar zareku: - 1. Aduwawa 2. Burji 3. Garko 4. Koya 5. Dangyatum 6. Muduga 7. San sani 8. Takalafiya 9. “Yanduma 10. Zareku Gari GUNDUMAR BASIRKA Garin Basirka garine mai tsohon tarihi da aka kafashi wajen shekara 1400AD. Asalin wanda suka kafa garin Maharbane kuma garin ya zama cibiyar kasuwancin wannan karkara wadda fatake ke Bullowa daga arewacin Africa don sayen Tufafi sakar Hausa su kuwa sukan kawo sukari da irin kayansu. Garin Basirka ya shahara wajen sana’ar saka da Runi. Kuma sunada manya da dadaddun karofi na tarihi, misali: - 1. Karofin Wudilawa dake tsakiyar Gari 2. Karofin Gandu dake gabas da Gari 3. karofin Kudu dake Kudu da Gari 4. Karofin Arewa dake Arewa da Gari 5. Karofin jike dake Unguwar Sabalari Basirka kuma garine daya zama hanyar Sojoji lokacin yakin Kamaru, kafin asamu isassun hanyoyin Mota na zamani, Fatake daga Gwambe, Biu, Yola duk tanan sukan bizuwa Kano akan Jakunansu da Dawakansu. Kuma da farko anyi niyyar Sarkin dawakin tsakar gida ya zama a Basirka amma daga baya sai ya zama a gwaram. Gidan da aka gina masa ya zama wajen saukar Sarki in yazo rangadi. Wannan yasa Basirka ta zama digaci karkashin Gwaram. WADANDA SUKAYI SARAUTA A BASIRKA 1. Sarkin Rugum 2. Sarki Jatau wadda ake yiwa Basirka lakabi dashi ake cewa Basirka garin HOHORI 3. Sarki Bawa Abubakar 4. Sarki Abdu Mafidi wanda Turawa suka nadoshi 5. Sarki Shehu 6. Sarki Ali Babar-bare 7. Sarki Ilyasu 8. Sarki Haruna 9. Sarki Garba Haruna A cikin shekara ta 2001 mai Martaba Sarkin Dutse ya Maida garin Basirka Gunduma ya tura Alhaji Ahmad Badayi Falakin Dutse a matsayin Hakimin basirka na farko, aka bashi wadannan Digatan: - 1. Basirka 2. Chediya 3. Chakwama 4. Digijin 5. Rabadi 6. Sagi 7. Matsango 8. T/Wadan kadale 9. Zambaram 10. Malaluwu 11. Kijin GUNDUMAR KIYAWATarihin garin Kiyawa ya samo asaline lokacin da wani Bafulatini mai suna Bokkoto, wadda ya fito daga Fika ta Jihar Borno, “Yobe a yanzu”, wadanda akace sun zauna a Dutse tare da dabbobinsu cikin shekara ta 1764. Ance a lokacin zamansa na Dutse Sarkin Kano Bello yanemi yayi sarautar Dutse amma Bokkoto yace shi bazaiyi sarauta ba yafison ya kula da dabbobinsa. Wannan yasa Bokkoto ya tafi gabas da Dutse tare da dabbobinsa don neman inda zai zauna yayi kiwon dabbobinsa. Akan hanyarsa yayi Zango a Zawaya wani wuri kusa da Fadamar Safa dake Kudu da garin Kiyawa na yanzu. A wannan wuri shanunsa sunyi kiwo sun sha Ruwa sun koshi sunyi tatil sai yace Kai !! da kyau. Wannan shine asalin sunan garin Kiyawa. Dan haka sai Bokkoto ya yanke shawarar zama a wannan wuri. Zaman Bokkoto a wannan wuri yaja hankalin mutane daga wurare daban daban suka runka tasowa daga lunguna suna zuwa garin Kiyawa da zama. Wannan yasa garin Kiyawa ya bunkasa. Kuma wadannan mutane suka nemi Bokkoto ya zama Shugabansu. Da farko Bokkoto yaki yarda sabo da dama tun fari ya taba yin haka a Dutse. Amma daga karshe Jama’a sun matsa masa ya yarda ya zama shugaban Kiyawa na farko. Kuma ya tsara yadda jama’a zasu zauna lafiya a tsakaninsu, kuma wadanda suka biyo bayansa suma sun hada kai da jama’arsu abin da yasa suka samu zaman lafiya da cigaban jama’arsu. Daga baya garin Kiyawa ya samu cigaba daga Sarautar Digaci zuwa na Hakimi, kuma ta koma Gunduma a shekara ta 1924. SUNAYEN WADANDA SUKA MULKI KASAR KIYAWA DAGA 1966 ZUWA 2003.
Kuma Mai karatu zaiga Kiyawa ta zama Gunduma Karkashin Hakiminta na farko Dan Lawan Umaru a shekara ta 1924, kuma daga baya ta koma matsayin Digaci a cikin shekara ta 1929. Wannan ya biyo bayan sake tsarin Gundumomi lokacin Turawa kafin asami mulkin kai. Kuma wanna tsari yaci gaba har zuwa 1976. A wannan lokaci aka sake samun Karin Hakimai a Kano, Kiyawa ta sake samun Hakimi aka nado Durbin Kano Alhaji Mai Kano Gwarzo amatsayin sabon Hakimin Kiyawa. Karamar hukumar Kiyawa data kunshi Gundumomin kiyawa da Shuwarin na alfahari da wadannan ‘ya’ya nata: - 1. Marigayi Alhaji Wada Abubakar – Tsohon Kwamishinan kasa da Safiyo a Jihar kano, Kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Shugaban kwamitin aikin Hajji a tarayyar Nigeria kuma Hakimin Kiyawa. 2. Alhaji Dan-Umma saleh – Tsohon malamin Makaranta, kuma tsohon Karamar Hukumar Kiyawa. 3. Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa – Tsohon Kwamishinan Ilmin Jihar Jigawa. 4. Dr. Yaro Kiyawa – Malamin Jami’a, tsohon wakili a kwamitin raba mukamai a tarayyar Nigeria 5. Alhaji Mustafa Makama - Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa, tsohon Kwamishinan kananan Hukumomin Jihar Jigawa kuma Shugaban Majalissar Jihar Jigawa. Shuwarin dacan Unguwace a karkashin digacin Gurduba wadda wani dalili yasa aka samu wani canji garin na gurduba yadawo yake bin Shuwarin. Asalin garin shuwarin ya samu sunansa daga wasu fulanin shuwa da suka zo daga wajen Borno sana’ar wadannan mutane itace saida Warwaro. Duk sanda mutane zasuje garin Shuwarin sai suce zamuje garin Shuwa-Shuwa musayo Warwaro wannan yasa aka hada Shuwa da Warwaro yazama shuwarin wato shuwa masu saida Warwaro. Garin na shuwa dacan karkashin gundumar Dutse yake kafin asamu takun saka tsakanin shugaban Karamar hukumar Dutse na farko Alhaji Basiru Dutse da Hakimin Dutse na wannan lokaci Alhaji Abdullahi Maikano Dutse. Alhaji Basiru ya maida Shuwarin karkashin Hakimin Kiyawa domin ya kare Mahaifinsa daga wulakanci a cikin shekara ta 1977 – 1978. Kafin shekara ta 2001 garin Shuwarin karkashin gundumar Kiyawa yake kuma anyi amfani da kasuwar shuwarin wajen neman Karamar Hukumar Kiyawa inda aka nunata wajen zamewarta babbar kasuwa da zata iya samawa Karamar hukumar ta Kiyawa da ake nema kudin shiga. A shekara ta 2001 cikin ikon Allah Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi ya daga Martabar shuwarin daga Digaci zuwa Hakimi karkashin shugabancin Alhaji Abubakar Abdullahi Sarkin Gabas. Gundumar shuwarin nada digatai kamar haka: - 1. Andaza 2. Akar 3. Garkon Alli 4. Duhuwa 5. Mazazzaga 6. Tsurma 7. Ciromawa 8. Gurm bayan gari 9. Kumi 10. Gurduba 11. Sabon gari 12. Shuwarin cikin gari WADANDA SUKA SHUGABANCI GARIN SHUWARIN. 1. Mallam Malli Mai-Unguwa 2. Mallam Abdulkadir “ 3. Mallam Malli II “ 4. Mallam Adamu “ 5. Mallam Usaini Adamu “ 6. Mallam Sule Adamu “ 7. Mallam Abdu gari “ 8. Alhaji Muhammdu Sanusi Digaci 9. Alhaji Amadu Badayi “ 10. Mallam sulaimanu Nahawwa Magajin garin Digaci 11. Alhaji Abubakar Abdullahi Hakimi GUNDUMAR GANTSAAn hada Tarihin Gantsa da wani Babban Tafkin Ruwa dake Arewa da garin wadda ake kira Shagari, ya kasance mashaya ga namun daji iri-iri. Hakan ya zamo yaja hankalin wani kasurgumun Maharbi Bafulatani mai suna Amadu ya maida wannan bakin ruwa wurin Kiiwo da Farauta, harma yaje ya jawo ‘yan uwansa suka maida wannan wuri a matsayin sansaninsu; Suka kafa garin awurin, suka kirashi Gantsa. Bayan kafa garin Gantsa sai Jama’a suka amince da shi Amadu ya zama Sarkinsu na farko a shekara 1801 – 1812. A zamanin Sarkin Fulani na hudu (4) “Sakamakon wata gwabzawa da akayi tsakanin dakarun Sarkin Kano Yusufu da Mutanen Gantsa, mulki ya koma hannun Habe a Shekara ta 1884. Wannan yaki yayi sanadin Rasuwar Sarkin Kano Yusufu sakamakon rauni da ya samu. Habe suka cigaba da mulkin Gantsa. A zamanin Sarkin Gantsa na biyar aka samu matsala ta tawaye daga Fulani. Wannan tirewa da ake samu ya tilasta aka maida mulki ga Sarakunan Fulani na farko sukaci gaba da mulkin Gantsa. Tun Sarkin Gantsa Dala har ya zuwa yanzu take hannun mulkin Fulani. Dagatan Gundumar Gantsa suna da kwakkwaran tarihi wajen kafuwarsu saboda kasancewar ada sun shiga yake-yaken basasa da manyan dakarun Sarakunan da sukayi fice wajen nuna jarinta. Wadannan sun hada da su Gwadayi, Yayarin Tukur, Kafin Madaki da dai sauransu. Manyan sana’oin Mutanen wannan gunduma sune Noma, Kamun Kifi, Saka, Ginin Tukwane, Kira da Kasuwanci. Wata babbar baiwa a tattare da wannan yanki shine duk da yake ta kasance a kan iyakar Jihohin Jigawa da Bauchi, jama’ar na zaune lafiya da juna. Kuma yankin ya kunshi kabilun Hausawa ,Fulani da Barebari da tsohon tarihi na baiwa da Allah yayiwa wannan yanki. Gundumar Hakimci, garin Gantsa ya zama Cibiyar Masarautar Hakimi a Shekara ta 2001 cikin watan hudu (AFRILU) kafin wannan matsayi na gundumar Hakimin a Gantsa shine Matawallen Dutse Alhaji Abubakar Bello. WADANDA SUKAYI MULKI A GANTSA
ADADIN DAGATAI DA MASU UNGUWANI
GUNDUMAR BUJITarihi ya nuna cewa an sami sunan garin Buji ne daga sunan wanda ya jagoranci kafa garin wato wani Bafulatani da ake kira Bubaji. Wanda Bubaji ya jagoranci ‘yan uwansu tun daga Bebeji ta kasar Kano don neman wurin dausayi dazai da ce dasu zauna da shanunsu. Sunan wata babbar Fadamar da a ke kira SHIWO shi yasa sukayi sansani suka kafa garin Buji. Garin Buji Allah ya albarkaceshi da jarimai wadda hakan yasa tun a zamanin yakin basasa sunsha gwabzawa da ayarin mayan Sarakuna kuma hakan yasa yankin ya fadada ta Fuskar mulki daga arewa da yakai har Kiyawa, Gabas har Jama’are da Gwaram. Da tafiya tayi tafiya, bayan yakin ba sasa. Anyiwa Buji a yaga zamanin Sarkin Kano Abbas inda aka kara garuruwan Gatsa, Gwadayi, Wurno, Chiirbun, Kiyawa, da Falagori. Buji ta shahara saboda Kasuwarta mai suna “LAHADIN BUJI” wadda jama’a na nesa kamar su Borno, Kano harma daga Agadas ake zuwa cin wannan kasuwa. Tarihin wannan gari ya kara fitowa fili a shekarar 1983 lokacin da aka kirkiro sabuwaR Karamar Hukumar Gantsa mai Cibiyar Mulki a Buji. Wannan tsari baiyi tsawon kwana ba domin wata uku kawai yayi aka rusheshi. Tarihi ya dada maimaita kansa a shekara 1996 lokacin da Gwamnatin Tarayya ta sake kirkiro da Karamar Hukumar Buji mai Cibiyar Mulki a Gantsa. Wannan ya kara habaka garin Buji har zuwa shekara 1998 sanda aka kirkiro gundumar Hakimin Buji aka kuma tura Hakimi na farko. Wannan yanki na Buji Allah ya albarkaceshi da Koguna da manyan Fadamu da kuma kasar Noma mai tarin albarka. Mutanen yankin mafiya rinjaye Fulanine da Hausawa da kuma Bare-Bari. Babbar sana’arsu itace Noma, Kamun Kifi da kuma kasuwanci. Akwai makarantu Firamare da Islamiyya da dama a wannan gunduma, kuma ana gudanar da Noman Rani sosai a wannan yanki. Haka zalika, Gundumar Buji tayi suna wajen samun ingantattun kuma rikakkun ‘yan Siyasa a Jiha da kasa baki daya. Bugu da kari, wannan yanki yakan zama mashekari ga dubban Fulani saboda wanzuwar zaman lafiya. Wato Bauran Dutse Alhaji Garba (Allah ya jikansa) Bayan rasuwarsa ne Mai Martaba Sarkin Dutse ya tura Matawallen Dutse Alhaji Abubakar Bello a shekarar 1999 kuma a wannan shekara ne jama’ar gundumar sukayi wani yunkuri don maida masalacin Buji irin na zamani karkashin jagorancin Dagacin Bujin Alhaji Umaru Lamido. A wannan hali da ake ciki, Gundumar Hakimin Buji ta hade dukkan yankin Karamar Hukamar nada har ya zuwa shekarar 2001 kuma shiyasa aka raba gundumar Buji da Gantsa, akabar Matwallen a sabuwar gundumar Gantsa kuma aka tura Katukan Dutse Alhaji Idris Fagam zuwa gundumar Buji a ranar 29/3/2001.
ADADIN DAGATAI DA MASU UNGUWANNI NA BUJI
Wannan Karamar Hukumar ta Buji mai cibiya a Gantsa ta kunshi Gundumomin Gantsa da Buji. Kuma tana Alfahari da ‘ya’yanta kamar su: - 1. Alhaji Abba Umar Kukuma – Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birnin kudu na farko, Kuma kwamashinan watsa labarai na Jihar Jigawa, kuma shugaban ma’aikatar jin koken Jama’ar jihar Jigawa (J.S.P.C.) 2. Alhaji Barau Abdullahi Gambasha - Tsohon Hedimasta, kuma Shugaban Karamar Hukumar Birnin kudu da Buji, dan malikin Dutse. 3. Alhaji Mika’ila – Darekta a Ma’aikatar mata ta Jihar Jigawa kuma Kantoman Birniwa. 4. Alhaji Hassan Gantsa – Darekta a Ma’aikatar daukar Ma’aikata ta Jihar Jigawa da ma’aikatar yada Addinin Muslinci ta Jihar Jigawa kuma tsohon Kantoman Karamar Hukumar Birniwa. 5. Alhaji Abdulkadir Aminu Gantsa – Tsohon ma kula da Ilmin Gundumar Ungoggo, kuma Naibin Limamin babban Masallacin Juma’a na Gantsa. Garin Basirka garine mai tsohon tarihi da aka kafashi wajen shekara 1400AD. Asalin wanda suka kafa garin Maharbane kuma garin ya zama cibiyar kasuwancin wannan karkara wadda fatake ke Bullowa daga arewacin Africa don sayen Tufafi sakar Hausa su kuwa sukan kawo sukari da irin kayansu. Garin Basirka ya shahara wajen sana’ar saka da Runi. Kuma sunada manya da dadaddun karofi na tarihi, misali: - 1. Karofin Wudilawa dake tsakiyar Gari 2. Karofin Gandu dake gabas da Gari 3. karofin Kudu dake Kudu da Gari 4. Karofin Arewa dake Arewa da Gari 5. Karofin jike dake Unguwar Sabalari Basirka kuma garine daya zama hanyar Sojoji lokacin yakin Kamaru, kafin asamu isassun hanyoyin Mota na zamani, Fatake daga Gwambe, Biu, Yola duk tanan sukan bizuwa Kano akan Jakunansu da Dawakansu. Kuma da farko anyi niyyar Sarkin dawakin tsakar gida ya zama a Basirka amma daga baya sai ya zama a gwaram. Gidan da aka gina masa ya zama wajen saukar Sarki in yazo rangadi. Wannan yasa Basirka ta zama digaci karkashin Gwaram. WADANDA SUKAYI SARAUTA A BASIRKA 1. Sarkin Rugum 2. Sarki Jatau wadda ake yiwa Basirka lakabi dashi ake cewa Basirka garin HOHORI 3. Sarki Bawa Abubakar 4. Sarki Abdu Mafidi wanda Turawa suka nadoshi 5. Sarki Shehu 6. Sarki Ali Babar-bare 7. Sarki Ilyasu 8. Sarki Haruna 9. Sarki Garba Haruna A cikin shekara ta 2001 mai Martaba Sarkin Dutse ya Maida garin Basirka Gunduma ya tura Alhaji Ahmad Badayi Falakin Dutse a matsayin Hakimin basirka na farko, aka bashi wadannan Digatan: - 1. Basirka 2. Chediya 3. Chakwama 4. Digijin 5. Rabadi 6. Sagi 7. Matsango 8. T/Wadan kadale 9. Zambaram 10. Malaluwu 11. Kijin
Anajin cewa wani mutum Bafulatani mai suna Abubakar Adamu (Masu Tarihi sun tabbatar da cewa Abubakar Adamu yana daya daga cikin 'yan sarautar Buji. A wannan da'awa Abubakar Adamu ya fito ne daga Buji ya fito ya sari Wurno) shine ya kafa garin Wurno a wajen shekara ta 1839. A lokacin da Abubakar yayiwo kaura zuwa wannan wurin an fara kiran sa da Bingingoda. A wani lokaci can kuma wani rukuni na bare-bari da suka fito daga balangori sunzo suma sun zauna a wannan wuri. Fulani da bare-bari sune manyan mazauna wannan Wurno. Shi kuwa sunan Wurno ya sami asaline daga wani mutum mai suna maiwurno wanda yazo daga garin Wurno kasar sakkwato da nufin Zuwa Makka, amma sai ya yada zango a wurin saboda karimcin da aka yi masa a matsayinsa na bako sai ya kira mutanen garin da cewa "Wurnan" da fulatanci wato wannan wuri ya zama gida a wajena. Maiwurno yaci gaba da zama a garin har sai da ya sami shekara daya kafin ya zarce zuwa Makka. To, a wannan rayuwa anan ganin wannan rayuwa wannan gari ya sami sunansa daga wannan mutum Maiwurno inda aka cigaba da kiran sa Wurno. Garin Wurno ya shahara sosai, ba safai ake iya cin su da yakiba. Ana jin ma Sarkin Ningi yasha kawo musu hari, amma bai yi nasaraba. Wurno ta zauna kasar dagaci shekaru da dama a karkashin hakimin Birnin kudu. Amma a shekara ta 2001, Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi Ya ciyar da Wurno gaba ta zama gundumar hakimi. Sarkin Yamman Dutse Alhaji Bashir Ahmad Aujara shi ne aka tura ya zama hakiminta na farko a ranar 23 ga watan maris na shekarar 2001. Garin Wurno ya sami cigaba ainun, musamman ta fuskar hadin kan jama'a da samun zaman lafiya. matasan kasar sun shiga ayyukan gwamnati daban-daban. Garin ya bunkasa kuma abubuwan zamani na kyautata jin dadin jama'a sun samu. Gundumar Wurno a yau tana da garuruwan dagatai kamar haka:
Sunayen wadanda suka riki Wurno a matsayin Digaci
MAJALISSUN KANANAN HUKUMOMIN MASARAUTAR DUTSE DA HAKIMANSU
|
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|