MASARAUTAR DUTSEDutse, Jihar Jigawa-Nigeria

Dutse a Yau
[Mafari] [Makunshi]

Sarkin Dutse Mai Daraja ta Daya Alhaji Dr. Nuhu Muhammadu Sanusi (1995 zuwa yau)

TSARIN ZAKKA A MASARAUTAR DUTSE

Sarki ya kirkiro yadda za’a karbi da yadda za’a raba Zakka daga hannun masu Dukiya zuwa mabukata guda takwas da Allah ya ambata a cikin Alkur’ani mai tSarki. Wannan tsari ya zama abin koyi domin Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki da yake a cikin tsarinsa akwai bin da kyautata dokokin Allah ya maida wannan shiri na zakka a Jihar Jigawa doka. Ya umarci dukkan Sarakunan Jihar Jigawa suyi koyi da Dutse. Sukafa ofisoshin zakka a majalissunsu. Dama shi Allah in kace da ruwanka dashi shima sai yayi ruwa dakai, ya taikama maka kan al’amuranka. Kuma ya saukaka maka wasu abubuwa masu wahala su saukaka.

 

TSARIN KWAMITOCIN KARBA DA RABA ZAKKA

 

Akowacce shekara Sarki yakan zabi garin da za’aje dan ganin yadda za’a fara rabon Zakkah kodai dan wannan Gari shi yafi tara zakka da yawa dan anuna godiya ga Hakimin ko kuma dan a nan aka samu mafi karancin Zakka damin Sarkin yanuna fushinsa ga wannan jama’a, kuma yayi musu huduba sannan a waje daya ya ja kunnan Hakimin kan sakacin da yayi wajen wannan aiki na Allah.

Wannan maganar zakka tasa kusan duk Jiholin Arewa harda zamfara da suka fara Shari’a sunzo MaSarautar Dutse sun sami ilimin yadda ake yin wannan aiki  na zakka cikin  nasara, harma da lokacin da wani daga cikin manyan malaman Nigeria yace da Sarkin Dutse, “Ranka yadade wannan tsari saikace ba’a Africa ba” !!

 

A SHEKARA TA 2000AD. LOKACIN DA AKA FARA WANNAN AIKIN ALHERI AN SAMU KAYA KAMAR HAKA  A MASARAUTAR DUTSE.

Nau’in Kwayoyi

1.                 A.      Hatsi Gero Dami 11,725

B.      Hatsi Gero Buhu 274

C.      Shinkafa Buhu 75

D.               Masara Buhu 8

2.       A.      Dawa  Dami  14, 168

B.                Dawa Buhu  481

C.               Gyada Buhu 435

D.               Wake Buhu 28

3.       Dabbobi

A.      Shanu Guda  14

B.      Tumaki Guda …..

C.      Awaki Guda 40

4.                 Kudi An sami Jimlar Kudi N 1,164, 990.00

 

ASHEKARA TA 2001 AD. AN TARA KAYA KAMAR HAKA BISA GA RAHOTON SHEKARAR.

1.         Hatsi-Nau’in Kwayoyi

A.               Gero Dami 22,220

B.                Gero Buhu 57+97

C.               Dawa Dami 15,589

D.               Dawa Buhu 299+126

E.                Wake Buhu 49 da shanshera kwano 144

F.                            Gyada Buhu 126+15

G.               Shinkafa Buhu 136+195 shanshera

H.               Masara Buhu 2

2.         Dabbobi

A.               Shanu guda 167

B.                Tumaki guda 105

C.               Awaki guda 30-(135)

3.         Kudi an tara kuma anraba N 1,434,700:00k

1.                 Hakimi 1st kyawa

2.                 Hakimi 2nd Gwaram

3.                 Hakimi 3rd Shuwarin.

 

RAHOTON ZAKKA NA SHEKARA TA 2002 YA NUNA AN SAMU KAYA KAMAR HAKA: -

1.       Hatsi Da Nauin Kwayoyi

1.                 Gero Dami 36,647

2.                 Gero Buhu 104 da kwano 20.

3.                 Dawa Dami 31,733

4.                 Dawa Buhu 435 da kwano 18.

5.                 Wake Buhu 7 da kwano 10.

6.                 Gyada Buhu 111 da kwano 16.5

7.                 Shinkafa Buhu 57 da kwano 37.

2.                 Dabbobi

1.                 Shanu guda 354

2.                 Tumaki guda –

3.                 Awaki guda 225

3        Kudi an tara kudi k uma an raba kudi

N       898,080:00

                         N       75, 458:000.00

JAWABIN ABINDA AKA SAMU A SHEKARA UKU (3) DA WADANDA AKA RABAWA

 

2000AD 1421AH

2001AD. 1422AH

2002AD. 1423AH

Miskinai

10,077

9,346

9,008

Fakirai

7,429

8,032

10,786

Saboda Allah

6,228

5,763

327

Masu aikin zakka

1,828

923

5,571

Matafiya

1,327

1,544

1,629

Wanda suka muslunta

 

 

 

 

[Makunshi] [Mafari]