MASARAUTAR DUTSE

Mafari
[Mafari] [Makunshi] [Dutse a Yau]

Manufar wanna bangare shine don biyan bukatar da manema tarihi suke da ita akan Dutse tun kafa Jihar Jigawa ta Nigeria mai cibiya a Dutsen. Dutse (Gadawur) boyayyen garine ga mutane da yawa in banda makaranta tun a tsohuwar Jihar Kano, don haka ya zamo abin mamaki sanda Shugaban kasar Nigeria Janar Ibrahim badamasi Babangida ya sanar da kirkirar Jihar Jigawa mai Babban birni a Dutse. Mutane da yawa sunyi suruce-suruce akan sa babban birnin jihar Jigawa a Dutse saboda a wannan lokacin a kwai manyan garuruwa kamar su Hadejia, Gumel da Kazaure a cikin Jihar.

Tarihi ya nuna  Dutse (Gadawur) na cikin garuruwa masu tarihi da za'a iya kwatance dasu a tsohuwar Jihar Kano, a hakikance ita kebin birnin Kano. Mazaunan Dutse sun zamo gwamutsen al'umma tun kafin karni na 15 a cikin su sun hada da Fulde (Genawa), kanuri (Wangarawa), Hausa (Digawa). Birnin Gija wanda yake kilomita kadan a yamma da garin Dutse sananne ne ga masana tarihi wajen kasuwanci a wajen birnin Kano. Yakin saifawa na El-kanemi ya kwace mulkin Gazargamu wanda ya janwo gudun hijirar fulani da yawa zuwa Dutse wanda suka kunshi kabilar Jalligawa da Yalligawa. 

Garin Dutse wanda yaci gaba da zama a gari marar yanci kafin jihadi, sanda sarakunan fulani sukai jabi ga malaminsu Sulaimanu sanda ya zamo Kalifa. Matsugunnin garin Dutse shi ya ba garin kariya da kuma damar koyar da mayakan garin cikin sirri.

Ina mai gayytarka ka shiga wannan shafi don sanin Tarihin wannan Gari, kana da damar bada Shawara ko gyara.

Gani da Ido
Tarihi

 

Don Shawara ko Gyara tuntubi Muhammad Araf